Labarin biloniya mai shekara 60 wanda ya tara sama da N380b kuma yake yawo a keke

Labarin biloniya mai shekara 60 wanda ya tara sama da N380b kuma yake yawo a keke

  • Marek Piechoki yana daga cikin wadanda ke da manyan hannun jari a LPP S.A kuma duk da kudinsa yake yawo a keke
  • Marek Piechocki ya kafa kasuwancin biliyoyin daloli amma yace ba zai sauya yadda yake tafiyar da rayuwarsa ba saboda kudi
  • Baya son fitowa cikin jama'a ko barakasa da kudi, har hotuna bayan dauka kuma baya kaunar a kirasa da attajiri

Babban attajiri kuma dan kasuwa, Marek Piechocki ya tallafa wurin kafa kasuwancin biliyoyin daloli amma dan kasuwar bai bar kudin da ya samu ya sauya masa rayuwa ba.

Shugaban kamfanin LPP S.A, wanda shine babban kamfanin samar da tufafi na kasar, yana gujewa jama'a kuma yana yawo a keke a maimakon motocin alfarma, Bloomberg ta ruwaito.

KU KARANTA: Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure

Labarin hamshakin mai kudi da ya tara arziki sama da biliyan N380 wanda ke yawo a keke
Labarin hamshakin mai kudi da ya tara arziki sama da biliyan N380 wanda ke yawo a keke. Hoto daga Simon Dowson
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita

Kamar yadda jerin biloniyoyin da Bloomberg ta bayyana, duk da gidauniyar gidansu, ya tara kudin da ya kai $1.1 biliyan.

Kamar yadda mai magana da yawun kamfanin tace, dan shekara 60 din ya jaddada cewa baya son a dinga kiransa da biloniya domin dukiyar ba tashi bace.

A 2018, ya tattara hannayen jarinsa inda ya mayar dasu gidauniyar, wacce yace da shi tare da sauran iyalan ne mallakinta.

An haramtawa gidauniyar siyar da hannayen jarin LLP.

"Yanayin tsarin mallakar kamfanin ya nuna cewa ba za a iya siyar da kamfanin nan kusa ba. A don haka, labari ne mai dadi ga wadanda ke aiki a karkashinsu," Slawomir Laboda, mataimakin shugaban kamfanin LPP ya sanar.

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta musanta rahoto dake yawo na cewa ta tura jami'an tsaro domin musgunawa dalibai masu zanga-zanga a kwalejin ilimi, wanda hakan ya janyo ajalin dalibi daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan yana zuwa ne bayan sa'o'i kadan da jami'an tsaro suka harbe wani dalibi daga cikin daruruwan dake zanga-zanga kan karin kudin makaranta.

A wani bayani ga manema labarai da kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan yayi, ya ce gwamnatin jihar Kaduna tana jiran bayanai domin su bata damar gano abinda ke kunshe a cikin rikicin da ya barke a Gidan Waya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng