Nnamdi Kanu na samun goyon bayan dillalan makamai na ƙasashen waje, Dattawan Arewa

Nnamdi Kanu na samun goyon bayan dillalan makamai na ƙasashen waje, Dattawan Arewa

  • Dattawan arewa sun gargadi gwamnatin tarayya ta yi takatsantsan da Nnamdi Kanu, suna mai cewa yana da abokan hulda a kasashen waje
  • Dattawan arewan sun sanar da hakan ne ta bakin mai magana da yawunsu, Mr Emmanuel Yawe
  • Kungiyar tana martani ne game da sake kama Kanu da aka yi daga kasar waje aka dawo da shi Nigeria ya fuskanci shari'a

Kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi takatsantsan da lamarin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, rahoton Daily Sun.

A cewar kungiyar ta Arewa, shugaban na masu fafutikan kafa kasar Biafra yana da abokan hulda sosai a kasashen ketare.

Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu na samun goyon bayan dillalan makamai na ƙasashen waje. Stefan Heunis/AFP

DUBA WANNAN: Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa a Kebbi Sun Sadaukar Da Rabin Albashinsu Don Yaƙar Ƴan Bindiga

Mai neman ballewa daga kasa da ke da magoya baya a kasashen waje

Kungiyar ta yi wannan furucin ne yayin da ta ke martani kan sake kama shugaban na IPOB a ranar Talata 29 ga watan Yuni.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa sakataren watsa labarai na ACF na kasa, Emmanuel Yawe yana cewa:

"Duba da sarkakiiyar da ke tattare da lamarin da abubuwan da ke faruwa a kasar game da wannan lamarin muna kira da gwamnati ta yi takatsantsan.
"Abin da ya fi dacewa shine a bi doka sau da kafa. Ya kamata a nuna wa Kanu da masu hada kai da shi cewa Nigeria ba kasa bace da ta gaza kuma akwai doka.

KU KARANTA: Fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamna Bala Mohammed sun mamaye birnin Kano

"Mun san cewa mutumin baya mutunta Nigeria kuma ya sha alwashin ruguza ta. Abin bakin ciki, wasu yan Nigeria da ke son ganin kasar ta ruguje na goyon bayansa.
"Yana kuma samun goyon baya daga dillalan makamai na kasashen waje da ke ganin yana iya janyo yaki ya barke a kasar Afirka mafi yawan jama'a da girman tattalin arziki."

An kama Nnamdi Kanu shugaban IPOB, an dawo da shi Nigeria

A bayan kun ji cewa an kama shugaban kungiyar masu fafutikan kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Amma News Wire ta ruwaito cewa ministan shari'a kuma Attoni Janar, Abubakar Malami ya tabbatarwa da hakan yana mai cewa an kama shi ne ranar Lahadi 27 ga watan Yuni kuma an dawo da shi Nigeria ya fuskanci shari'a.

Ya ce an kama shi ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaron Nigeria da yan sandan kasa da kasa Interpol.

Asali: Legit.ng

Online view pixel