Dattijuwa mai shekaru 55 tayi haihuwar farko, mijinta ya tsere, ta samu kyautar N400K

Dattijuwa mai shekaru 55 tayi haihuwar farko, mijinta ya tsere, ta samu kyautar N400K

  • Wata mata dattijuwa 'yar Najeriya mai shekaru 55 ta haihu a cikin kwanakin nan karo na farko
  • Amma kuma sai mijinta ya tsere ya bar ta saboda ba zai iya biyan kudin asibiti ba na haihuwar
  • Abun mamaki shine yadda ta rasa mahaifarta yayin haihuwar amma wasu suka bata kyautar N400K, wani kuma ya biya kudin asibiti

Wata dattijuwar mata 'yar Najeriya ta haihu yayin da take shekara 55 a duniya kuma wannan haihuwar ce ta fako.

Sai dai matar mai shekaru 55 ta shiga tashin hankula har biyu a yayin da ta samu farin cikin haihuwar da tayi.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama jami'in dake karbar rashawa da bukatar kwanciya da masu laifi

Dattijuwa mai shekaru 55 tayi haihuwar farko, mijinta ya tsere, ta samu kyautar N400K
Dattijuwa mai shekaru 55 tayi haihuwar farko, mijinta ya tsere, ta samu kyautar N400K. Hoto daga @gsf
Asali: Instagram

KU KARANTA: Na shirya baiwa Fulani filayen kiwo a jihata, Gwamna Ortom

Kamar yadda @kingtundedednut wanda ya sake wallafa labarin a Instagram ya sanar, mijin matar ya tsere ya bar ta a asibiti saboda yawan kudin da aka bukata kuma ta rasa mahaifarta.

Taimako ya zo ta inda ba a tsammani

Taimako ya zo wa matar ta karkashin gidauniyar Givers Supportive Foundation, kungiyar taimakon kai da kai.

Kungiyar ta wallafa bidiyon a shafinta na Instagram inda tace ta ziyarci matar a asibitin da ta haihu. Sun biya kudin kuma aka bata kyautar N400,000.

Matar ta kasa boye farin cikinta yayin da take godiya ga kungiyar. 'Yan Najeriya sun dinga jinjinawa taimakon da gidauniyar tayi wa matar tare da yi wa matar fatan alheri.

Ga tsokaci da jinjinar 'yan Najeriya

@adebimpe_samafaajinternational tsokaci tayi da: "Sannunku da aiki kuma Allah yayi muku albarka dukkanku."

@samuelolufemi5 cewa yayi: "Ubangiji zai cigaba da karafafa ku."

@follyzhair ta ce: "Allah yayi muku albarka tare da wadanda suka bada gudumawarsu."

@olivetoshine ta ce: "Kai, Allah kayi min albarka, akwai bukatar in dinga bada gudumawata ga ire-iren wadannan."

@starkeskate cewa yayi: "A gaskiya wannan zance ne mai dadi. Ubangiji nake fata ya cigaba da kula da yaron."

A wani labari na daban, kwamitin ayyuka na jami'yyar PDP ya kira taron gaggawa a yau Litinin domin tattaunawa kan sauya shekar da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle zai yi zuwa jam'iyyar APC.

Kamar yadda ThisDay ta ruwaito, a wani sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara ya fitar, ya ce suna gayyatar gwamnoni masu goyon baya don su halarci sauya shekar.

Takardar ta kara da cewa, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje tare da wasu jiga-jigan APC zasu karba gwamnan jihar Zamfaran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng