Nnamdi Kanu: Kada gwamnatin tarayya ta kuskura ta cutar da shi – Tsohon minista Amechi ya yi martani

Nnamdi Kanu: Kada gwamnatin tarayya ta kuskura ta cutar da shi – Tsohon minista Amechi ya yi martani

  • Martani na ci gaba da billowa kan kame Mazi Nnamdi Kanu, wani madugun 'yan aware da aka yi
  • Gwamnatin Najeriya ta sanar da kamun na Kanu a ranar Talata, 29 ga watan Yuni ta bakin babban jami’in shari’ar kasar
  • Wani dattijo dan yankin kudu maso gabas inda Kanu ya fito, ya ce ya kamata a ba wa dan rajin ballewar damar jin ta bakinsa

Wani dattijon kasa kuma ministan sifirin jiragen sama na jamhuriya ta biyu, Mbazulike Amechi, ya fadawa gwamnatin tarayya da ta yi wa shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu adalci.

Amechi, a wata hira da jaridar Daily Sun a ranar Talata, 29 ga watan Yuni, ya ce kamata ya yi a dauki Kanu a matsayin mara laifi har sai kotun da ke da hurumi ta same shi da laifi.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunaye da hotunan gwamnonin APC da ke Zamfara a yanzu haka don sauyin shekar Matawalle

Nnamdi Kanu: Kada gwamnatin tarayya ta kuskura ta cutar da shi – Tsohon minista Amechi ya yi martani
Tsohon minista Amechi ya bukaci FG da ta ba Nnamdi Kanu dama a ji ta bakin shi Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Maganar gargadi ga gwamnatin tarayya

Kalmominsa:

“Shawarata ita ce, ya kamata hukumomin tarayya su yi taka-tsantsan kan yadda za su tafiyar da Nnamdi Kanu, da kuma yadda za su bi da shari’arsa.
“Da farko, kada su tsare shi ba tare da wani dalili ba. Su kai shi kotu, su gabatar da kararsa, kuma idan aka same shi da laifi, doka za ta fayyace abin da za a yi da shi.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Mahdi kan zargin batanci ga Masari

“Amma ya zama dole kada hukumomi su cutar da shi ko kuma su tsare shi har sai baba-ta-gani a kurkukun su; saboda shi mutum ne. Dole ne a ba shi damar samun lauyan da zai kare shi.”

Kotu ta amince hukumar DSS ta tsare Nnamdi Kanu zuwa watan Yuli

A gefe guda, babban kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja ta bada umurnin a ajiye mata shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a hannun hukumar tsaron farin kaya DSS har zuwa ranar 26 ga watan Yuli, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton The Cable an kama Kanu ne a kasar waje aka dawo da shi Nigeria a jirgin sama a ranar Lahadi.

An sake gurfanar da shi gaban Mai shari'a Binta Nyako a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel