Da Ɗuminsa: Kotu ta amince hukumar DSS ta tsare Nnamdi Kanu zuwa watan Yuli

Da Ɗuminsa: Kotu ta amince hukumar DSS ta tsare Nnamdi Kanu zuwa watan Yuli

  • Kotu ta bada umurnin hukumar tsaron farin kaya, DSS, ta ajiye mata Nnamdi Kanu har zuwa ranar 26 ga watan Yuli
  • Mai shari'a Binta Nyako ce ta bada umurnin bayan lauya mai wakiltar attoni janar ya gabatarwa kotun bukatar
  • Tunda farko dai Mai shari'a Binta Nyako ce ta bada belin Nnamdi Kanu kan dalilin rashin lafiya amma daga bisani ya tsere ya bar kasar

Babban kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja ta bada umurnin a ajiye mata shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu a hannun hukumar tsaron farin kaya DSS har zuwa ranar 26 ga watan Yuli, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton The Cable an kama Kanu ne a kasar waje aka dawo da shi Nigeria a jirgin sama a ranar Lahadi.

Kotu ta ce a ajiye Nnamdi Kanu a hannun DSS
Kotu ta ce a ajiye Nnamdi Kanu a hannun DSS. Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamna Bala Mohammed sun mamaye birnin Kano

An sake gurfanar da shi gaban Mai shari'a Binta Nyako a ranar Talata.

Nyako ce alkalin da ta bada belinsa bisa rashin lafiya a shekarar 2017.

Kanu ya saba dokokin belinsa ya tsere, hakan yasa alkalin ta janye belin daga bisani.

Ya samu ya tsere zuwa kasar waje inda ya cigaba da ingiza mabiyansa da ke kungiyar tsaro ta yankin kudu wato ESN.

KU KARANTA: An kama garada 3 da suka ɗirka wa matar aure ciki kafin shigar da ita 'Ɗarikar Haƙiƙa' a Katsina

A ranar Talata, Lauya Attoni Janar na kasa kuma ministan shari'a, Shuaibu Labaran ya shaidawa kotu cewa an kamo Kanu sannan aka kawo shi kotu.

Labaran ya bukaci kotun ta bada umurnin a tsare Kanu a hannun hukumar tsaron farin kaya DSS kafin zuwa ranar da za a saurari shari'arsa.

Mai shari'a Nyako ta amince da hakan, ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 26 ga watan Yulin 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164