Karin bayani: Gwamnoni sun isa fadar sarkin Kano don tsara bikin Yusuf Buhari

Karin bayani: Gwamnoni sun isa fadar sarkin Kano don tsara bikin Yusuf Buhari

  • A yau ne gwamoni da manyan 'yan siyasar Najeriya suka hallara a gidan mai martaba sarkin Kano
  • Sun bayyana a gidan ne don sanya ranar auren dan shugaba Buhari da 'yar sarkin Biki a jihar Kano
  • Shugaba Buhari ne ya tura tawagar, wacce ta zauna zaman tsara shirin bikin da zai gudana nan gaba

Gwamnoni da ministoci a halin yanzu sun isa fadar mai martaba Sarkin Kano don tsara tsare-tsaren bikin auren Yusuf Buhari, dan shugaban kasa, Daily Trust ta ruwaito.

A yanzu haka Yusuf na shirin auren diyar Sarkin Bichi kuma tawagar da ke karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa suna Kano don tsara tsare-tsaren bikin auren.

Sarkin na Bichi kane ne ga Sarkin Kano, wanda a yanzu haka shi ke karbar bakuncin wakilai daga fadar shugaban kasa.

KU KARANTA: Bayan Gwamna Matawalle, Jigo a Jam'iyyar APGA Ya Bi Sahu Zuwa Jam'iyyar APC

Yanzun nan: Gwamnoni sun dira fadar sarkin Kano da nufin tsara bikin Yusuf Buhari
Yusuf Buhari, dan shugaban kasar Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com

Rahoto ya bayyana cewa, iyalai da kusa da nesa sun taru don tsara bikin wanda ake sa ran zai gudana tsakanin watan Agusta da Satumban bana.

Gwamnoni da suka hada da Atiku Bagudu na jihar Kebbi da Babagana Zulum na jihar Borno suna cikin tawagar da ta hada da Mataimakin Gwamna Nasir Gawuna na Jihar Kano.

Tsoffin gwamnoni Abdulaziz Yari (Zamfara), Ali Modu Sherif (Borno) da Ibikunle Amosun (Ogun) duk suna fadar tare da Abubakar Malami (SAN), Babban Lauyan Tarayya.

Buhari ne ya tura tawaga gidan Sarkin Bichi don sa ranar auren 'dansa Yusuf

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika tawagar wakilansa domin ganawa da iyalan Sarkin Bichi kan sa ranar daurin auren 'dansa, Yusuf Buhari, da Zahra Bayero.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa wannan tawagar da Buhari ya tura ta hada da gwamnoni, Ministoci, da Dirakta Janar da hukumar DSS, Yusuf Bichi.

An tattaro cewa tuni wasu sun dira jihar Kano da kayayyakin sa rana irinsu goro, da sauransu.

Hakazalika an shirya ganawar tawagar da dattijon gidan Bayero, Idris Bayero, da Sarkin Kano, Aminu Bayero, ranar Lahadi.

KU KARANTA: Tsohon shugaba Jonathan ya magantu kan abinda ke jawo aikata laifuka a Najeriya

A wani labarin, Wata budurwa 'yar Najeriya ta gigita kafafen sada zumunta bayan ta amince da tayin auren saurayinta.

Matar mai amfani da @swiss_scarlet a Instagram, ta wallafa wani bidiyo inda saurayinta ya gwangwajeta da N2.5 miliyan saboda ta amince da tayin aurensa.

Kamar yadda Instabog9ja ta tabbatar, budurwar masaniya ce a fannin hada mayuka. A wani bidiyo dake yawo, an boye fuskar saurayin sai dai hannunsa kadai ake iya gani inda yake zuba mata ruwan lemu a kofi tare da saka mata zobe a hannu.

Budurwar cike da jin dadi tare da annashuwa ta nuna mamakinta game da dunkulin kudin da aka bata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel