Hankula sun tashi a Legas bayan Sunday Igboho ya sha alwashin gangami a jihar

Hankula sun tashi a Legas bayan Sunday Igboho ya sha alwashin gangami a jihar

  • Hankulan jama'a mazauna jihar Legas ya fara tashi bayan masu rajin neman kasar Yarabawa sun sha alwashin yin gangami a jihar
  • Kamar yadda shugaban tafiyar, Sunday Igboho ya sanar, yace babu gudu balle ja da baya, 3 ga watan Yuli zasu yi gangamin
  • Kungiyar Yarabawa karkashin Farfesa Akintoye tayi kira ga yarabawa da su fito kwansu da kwarkwatarsu

Hankula sun fara tashi a jihar Legas sakamakon shirin gangamin kafa kasar yarabawa da ake shirin yi ranar 3 ga watan Yuli wanda zai samu shugabancin Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

Igboho yayi makamancin wannan gangamin a jihohin Ogun, Oyo, Ekiti, Osun da Ondo, Daily Trust ta ruwaito.

Bayan zanga-zangar EndSARS da aka yi a shekarar da ta gabata wacce ta kai ga asarar kadarorin gwamnati, hukumomin sun kasance a ankare game da gangamin da zai kai ga tashin hankula tare da karya doka.

KU KARANTA: Na shirya baiwa Fulani filayen kiwo a jihata, Gwamna Ortom

Hankula sun tashi a Legas bayan Igboho ya sha alwashin zanga-zanga a jihar
Hankula sun tashi a Legas bayan Igboho ya sha alwashin zanga-zanga a jihar. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: PDP ta kira taron gaggawa bayan wani gwamna na kokarin komawa APC

A shirin gangamin na kasar Yarabawa, mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Muyiwa Adejobi ya sanar da Daily Trust cewa "Rundunar za ta yi martani kan gangamin a lokacin da ya dace."

Wasu shugabannin a jihar da aka tuntuba a ranar Litinin sun ki tsokaci amma sun bayyana damuwarsu kan gangamin saboda zai iya jefa jihar cikin wani hali.

"Amma dai muna bukatar addu'a ga kasar nan ta yadda zamu tsallake wadannan kalubalen. Wannan kalubalen na wucin-gadi ne wanda babu shakka zai wuce," daya daga cikin shugabannin yace.

Ilana Omo Oodua, wata kungiyar Yarabawa karkashin shugabancin Farfesan tarihi, Banji Akintoye, sun goyi bayan gangamin inda suka yi kira ga 'ya'yan Yarabawa da su fito kwan su da kwarkwatarsu.

A wata takarda da babban sakatarensu George Akinola ya fitar, ya ce kungiyar ta ce hatta daga kasashen ketare za a duba gangamin.

A wani labari na daban, manyan masu mukaman siyasa wadanda suka wakilci fadar shugaban kasa sun isa fadar sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero domin nemawa da daya tilo na shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari aure.

Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru, ya jagoranci wakilan zuwa fadar a ranar Lahadi, 27 ga watan Yuni tare da wasu gwamnoni da manyan jami'an gwamnati da suka hada da ministan shari'a, Abubakar Malami, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

An sanya ranar auren Yusuf da Zahra Bayero, diyar sarkin Bichi, Alhaji Dr. Nasir Bayero, mai shekaru 19 a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel