'Yan sanda sun kama jami'in dake karbar rashawa da bukatar kwanciya da masu laifi

'Yan sanda sun kama jami'in dake karbar rashawa da bukatar kwanciya da masu laifi

  • Rundunar 'yan sandan Akwa Ibom ta damke wani jami'in dan sanda kan zargin karbar kudi da bukatar kwanciya da masu laifi
  • A wani bidiyo da ya yadu, an ga jami'in mai suna Daniel Edet yana bukatar karbar N60,000 tare da kwanciya da wata mai laifi
  • Tuni kwamishinan 'yan sandan jihar ya bada umarnin kama shi da kuma shugabansa sannan a tsananta bincike

Rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom ta bada umarnin kama wani dan sanda a kan zarginsa da ake da karbar kudi hannun mutane tare da bukatar kwanciya da wadanda ake zargi.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Akwa Ibom, Odiko Macdon, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar ga manema labarai a Uyo ranar Lahadi.

Macdon, dan sanda mai mukamin SP ya ce wannan abun da dan sanda yake yi an gano ne bayan wani Zion Umoh ya nadi bidiyon yayin da dan sandan mai suna Daniel Edet ke bukatar lalata da kuma karbar N60,000 daga wacce ake zargi.

KU KARANTA: Amurka: An yankewa dan sandan da ya kashe bakar fata Floyd shekaru 22.5 a gidan yari

'Yan sanda sun kama jami'in dake karbar rashawa da bukatar kwanciya da masu laifi
'Yan sanda sun kama jami'in dake karbar rashawa da bukatar kwanciya da masu laifi. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: APC ta dawo kamar yadda take da, Buhari yace rikicin jam'iyya ya kare

Kamar yadda Guardian ta wallafa, saboda wannan zargin, kwamishinan 'yan sandan jihar Akwa Ibom, CP Andrew Amiengheme, ya bada umarnin kamawa tare da bincikar jami'in dan sandan.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce matukar aka tabbatar da laifin dan sandan, dole ne ya fuskanci hukunci.

Macdon ya ce, "An sanar da rundunar 'yan sandan wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta wanda wani Zion Umoh ya wallafa.

"A bidiyon an ga wani dan sanda mai suna Daniel Edet dake aiki da yankin Etim Ekpo yana bukatar lalata da karbar N60,000 daga wacce ake zargi a matsayin beli.

"Nauyin wannan zargin yasa kwamishinan 'yan sandan jihar ya bada umarnin kama jami'in da kuma ogan shi na wurin aiki.

“Ya bada umarnin bincike mai tsanani tare da daukar mataki na ladabtarwa ga jami'in idan akwai bukatar hakan."

A wani labari na daban, kungiyar tsageru ta Niger Delta Avengers, wacce aka sani da tada kayar baya a yankin Niger Delta yayin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na farko, sun sanar da dawowarsu, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Idan za a tuna, kungiyar ta gurgunta tattalin arzikin Najeriya daga 2016 zuwa 2018 ta hanyar kai farmaki wuraren diban man fetur dake yankin, lamarin da yasa kasar Najeriya ta fada karayar tattalin arziki.

A wata takarda da suka baiwa manema labarai a ranar Asabar, kungiyar tsagerun ta ce ta kaddamar da 'Operation Humble' wanda take son amfani dashi wurin gurgunta tattalin arzikin kasar nan kamar yadda tayi a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel