Mutum ɗaya ya mutu, da dama sun jikkata a harin da 'dodo' ya kai wa masallata a Osun
- An kai hari wani masallaci a Osogbo inda aka jikkata mutane da dama yayin da suke gudanar da ibada
- Wani dodo da mabiyansa ne ake zargi da kai harin wanda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutum daya
- Ba a samu ji ta bakin rundunar yan sandan Jihar Osun ba har zuwa hada wannan rahoton
Akalla mutum daya aka harbe har lahira yayin da masu gudanar da ibada da dama suka jikkata a wani hari da aka kai masallaci a Osogbo, babban birnin Jihar Osun, Daily Trust ta ruwaito.
Wani dodo da mabiyansa ne ake zargi da alhakin kai harin a harabar massallaci, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum guda mai suna Moshood Salawudeen.
DUBA WANNAN: An kama garada 3 da suka ɗirka wa matar aure ciki kafin shigar da ita 'Ɗarikar Haƙiƙa' a Katsina
The Punch ta ruwaito cewa harin ya faru ne yayin da masu bautar ke gabatar da sallah a karkashin rumfa ranar Lahadi.
Maharan sun wuce ta gidan Oluade Arayin, inda masallacin yake.
An ruwaito cewa sun lalata kofofi da tagogin masallacin a harin.
A cewar babban limamin masallacin, Alhaji Quoseem Yunus, babu wani sabani tsakanin su da dodon.
Ya ce dodon da mabiyansa sun wuce ta yankin a karon farko ba tare da sun farmaki masu bautar ba.
DUBA WANNAN: Zarah Ado Bayero: Abin da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano da Yusuf Buhari zai aura
Yunus ya ce suna wajen masallacin, suna gudanar da addu'o'i na musamman lokacin da dodon da mutanen sa suka bayyana.
Wanda suka ji rauni suna kwance a asibitin Jiha, Osogbo, su kuma wanda suka mutu suna dakin adana gawa.
Ba a samu jin ta bakin rundunar yan sandan jihar ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu
A wani labarin, kun ji wani mutum mai shekaru 40, Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.
Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.
Ya shaidawa kotu cewa mahaifinsu da Allah ya yi wa rasuwa ya bar wasiyya cewa a mayar da ɗaya daga ɗakunan gidan zuwa masallaci amma wadanda ya yi ƙarar sun saɓa umurnin mahaifin a cewar rahoton na Vanguard.
Asali: Legit.ng