An kama garada 3 da suka ɗirka wa matar aure ciki kafin shigar da ita 'Ɗarikar Haƙiƙa' a Katsina

An kama garada 3 da suka ɗirka wa matar aure ciki kafin shigar da ita 'Ɗarikar Haƙiƙa' a Katsina

  • Wasu matasa uku sun dirkawa wata matar aure ciki kafin su shigar da ita wata darika a Katsina
  • Mijin matar ne ya shigar da korafi bayan shafe shekara guda baya gida kuma ya dawo ya tarar da matar tasa da jaririyar wata hudu
  • Matasan sun bayyana kwanciya da ita a matsayin sharadin shiga Hakikar kuma ta amince su ukun suka kwanta da ita

'Yan sanda a Jihar Katsina sun cafke wasu mutane uku mabiya addinin musulunci masu bin Darikar Hakika bisa haduwa tare da yiwa wata matar aure ciki a karkashin ka'idojin shiga darikar.

A wata sanarwa, rundunar yan sandan tace mijin matar ne ya shigar da korafi gaban hukumar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito

Matasa uku da suka yi wa wata mata ciki a Katsina
Matasa uku da suka yi wa wata mata ciki a Katsina. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

LIB ta ruwaito cewa Isiyaku ya dawo daga Lagos bayan shafe shekara daya kuma ya iske matar sa da jaririn wata hudu.

DUBA WANNAN: Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

Ya damka amanar matarsa, Zainab Ahmad, a hannun iyayen ta dake garin Dantalle, Tandama, Karamar hukumar Danja a Jihar Katsina.

Daga bisani ne aka gano wasu 'yan hakika' guda uku a kauyen ne suka yi mata wayo suka kuma yi mata ciki.

Da yan sanda suke tuhumar ta, Zainab ta tabbatar da cewa ita ta nuna sha'awar shiga darikar, sai suka karanta min sharadin cewa sai sun kwanta dani kafin su sakani.

Na amince musu kuma duka su ukun sun kwanta dani, sai suka sakani a darikar tasu.

KU KARANTA: 'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika

Rahoton yan sandan ya ce, "a cikin karar, wani Abdullahi Isiyaku mai shekaru 30 dan kauyen Wardanga a karamar hukumar Bakori da ke Jihar Katsina ya kai korafi ofishin yan sanda da ke Danja ranar 17 ga watan Yuni, 2021, cewa a watan Janairun 2021, yayi tafiya zuwa Lagos kuma ya bar matarsa, Zainab Ahmad mai shekaru 20, karkashin kulawar iyayen ta a Unguwar Dantalle ta kauyen Tandama a karamar hukumar Danja ta Jihar Katsina.
"Sai dai, bayan dawowar sa a farkon watan Yuni, ya iske matar sa da jaririya mace yar kimanin wata hudu. Da aka gudanar da bincike, matar ta bayyana cewa ta shiga sabuwar darika da ake kira 'Hakika' ta hannun wasu matasa uku da ake zargin masu fyade ne wanda suka hadu suka kwanta da ita.
"Wanda ake zargin - Tukur Dan-Azumi, mai shekaru 19, Abubakar Yahuza, mai shekaru 20, Rufa'i Saosi, mai shekaru 27 duka daga Unguwar Dantalle a kauyen Tandama da ke Danja."

Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

A wani labarin, kun ji wani mutum mai shekaru 40, Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.

Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.

Ya shaidawa kotu cewa mahaifinsu da Allah ya yi wa rasuwa ya bar wasiyya cewa a mayar da ɗaya daga ɗakunan gidan zuwa masallaci amma wadanda ya yi ƙarar sun saɓa umurnin mahaifin a cewar rahoton na Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel