Gwarazan Sojoji Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Fatattake su a Jihar Kaduna

Gwarazan Sojoji Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Fatattake su a Jihar Kaduna

  • Gwarazan sojoji a kudancin Kaduna, sun samu nasarar daƙile harin wasu yan bindiga a Gidan zaki, ƙaramar hukumar Zangon Kataf
  • Yan bindigan sun kai hari ƙauyen, inda suka fara lalata gidan wani mazaunin garin tare da wata mota dake kusa
  • Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna ya nuna matuƙar damuwarsa a kan faruwar lamarin

Jami'an soji na hedkwatar tsaro ta rundunar Operation Save Haven dake kudancin Kaduna sun daƙile harin yan bindiga a ƙauyen Gidan Zaki, ƙaramar hukumar Zangon Kataf, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Har Yanzun Akwai Yankunan Dake Hannun Yan Ta'adda, Shehun Borno Ga Sabon COAS

Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, shine ya faɗi haka ranar Lahadi.

Yace yan bindigan sun fara mamaye gonakin ƙauyen, inda suka girbe shukar Masarar mutanen ƙauyen da adduna.

Sojoji sun daƙile harin yan bindiga a Kaduna
Gwarazan Sojoji Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Fatattake su a Jihar Kaduna Hoto: vangauardngr.com
Asali: UGC

Yace: "Yan bindigan sun lalata gidan ɗaya daga cikin mazauna ƙauyen, Mr Joseph Aboi. Sanan suka lalata wata mota dake kusa da gidan, daga baya kuma suka farmaki wani shagon cajin waya suka sace wayoyi."

"Nan da nan jami'an soji suka kawo ɗauki, inda suka fatattaki maharan cikin ƙanƙanin lokaci. Wata yar ƙauyen mai suna Angelina Francis, ta samu raunin harbi yayin da yan bindigan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, amma an kaita wani asibiti mafi kusa."

KARANTA ANAN: Babu Wanɗanda Suka Dace da Mulkin Najeriya a 2023 Fiye da Tinubu/Ganduje, Inji TPN

Gwamna El-Rufa'i ya nuna damuwarsa da kai harin

Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya nuna rashin jin daɗinsa da kai wannan hari, yayin da ya jinjina wa sojoji bisa daƙile harin tun kafin yayi muni.

Aruwan, yace: "Gwamna El-Rufa'i ya nuna damuwarsa da kai harin, kuma ya jinjinawa jam'ian soji bisa kai ɗauki da suka yi, har suka daƙile harin."

"Gwamnan yayi fatan samun lafiya cikin gaggawa ga waɗanda suka samu raunuka yayin harin."

A wani labarin kuma Danbarwa Ta Ɓarke a Jam'iyyar APC Bayan Sanar da Ɗan Takarar Gwamna a Zaɓen Dake Tafe

Danbarwa ta ɓarke a jam'iyyar APC reshen jihar Anambra biyo bayan bayyana wanda ya lashe zaɓen fitar da ɗan takara, kamae yadda punch ta ruwaito.

Ministan ƙwadugo, Chris Ngige, yace kwata-kwata ba'a gudanar da wani zaɓe ba a jihar, ya kuma bada shawarar 29 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262