COAS Ya Sake Kai Ziyara Borno, Ya Umarci Sojoji Su Ragargaji Yan Boko Haram da ISWAP
- Hafsan sojin ƙasa, COAS Farouƙ Yahaya, ya umarci rundunar sojin dake yaƙi a arewa maso gabas da su kawo ƙarshen ta'addanci
- Mr. Yahaya yayi wannan roƙon ne yayin da yakai wata ziyarar aiki ga rundunar operation haɗin kai a Monguno
- Shugaban Sojin ya kuma kai ziyara fadar mai martaba shehun Borno, inda ya nemi haɗin kan sarakuna
Shugaban rundunar sojin ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya umarci jami'an operation haɗin kai (OPHK) da su kasance koda yaushe a cikin shirin ko ta kwana da harin yan ta'adda da masu tada ƙayar baya a yankin arewa maso gabas, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Gwarazan Sojoji Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Fatattake su a Jihar Kaduna
Mr. Yahaya ya yi wannan umarnin ne yayin wata ziyarar aiki da ya kaiwa rundunar sashi na 3 na Operation haɗin kai dake Monguno, waɗanda ke yaƙi da yan Boko Haram da ISWAP.
Kakakin rundunar soji, Onyema Nwachukwu, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi.
Mr. Nwachukwu, yace: "COAS ya nuna tsantsar jin daɗinsa kan yadda sojoji ke samun nasara a yaƙin da suke yi da yan ta'adda a yankin arewa maso gabas."
"Ya umarci jami'an da su cigaba da wannan kokarin, sannan su kasance cikin shiri a koda yaushe. Ya kuma roƙi sojojin su riƙa amfani da dabaru yayin gudanar da operation a kowane lokaci."
Shuagaban sojin ya kuma yi kira ga jami'an su cigaba da daukar mataki yadda ya kamata domin kawo ƙarshen aikin ta'addanci a yankin.
KARANTA ANAN: Har Yanzun Akwai Yankunan Dake Hannun Yan Ta'adda, Shehun Borno Ga Sabon COAS
COAS ya kai ziyara fadar mai martaba Shehun Borno
Yayin ziyarar da yakai fadar mai martaba shehun Borno, Yahaya ya nemi sarakuna da su baiwa jami'an soji haɗin kai a yaƙin da suke yi, kamar yadda premium times ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa matuƙar aka samu alaƙa mai kyau tsakanin jami'an tsaro da sarakuna, to cikin ƙanƙanin lokaci za'a kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.
A wani labarin kuma Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhari
Shugaba Buhari ya ƙara jaddada maganarsa kan cewa duk wanda ya ɗauki makami ya yaƙi Najeriya zai fuskanci hukunci.
Shugaban yace matasa na da rawar da zasu taka domin gina goben su da kuma ƙasar su.
Asali: Legit.ng