Lauya ya yi karar Buhari a kotu saboda yawan zuwa asibitocin waje da yake yi neman lafiya

Lauya ya yi karar Buhari a kotu saboda yawan zuwa asibitocin waje da yake yi neman lafiya

  • Deji Enisenyin ya je kotu ya na so a haramta fita waje da Shugaban Najeriya ya ke yi
  • Lauyan ya ce Muhammadu Buhari ya na saba dokar kiwon lafiya da aka kawo a 2014

Wani Lauya mai suna Deji Enisenyin, ya shigar da karar shugaba Muhammadu Buhari a kotu, a kan yawan fita kasashen waje da yake yi domin ganin likita.

Jaridar Sun ta ce wannan lauyan ya na ikirarin cewa ziryar da shugaban kasar Najeriyar yake yi a asibitocin ketaren, ya saba wa dokar lafiya ta kasa ta 2014.

Rahotan ya bayyana cewa Deji Enisenyin ya kai kara ne mai lamba FHC/AB/CS/51/21 a babban kotun tarayya da ke garin Abeokuta, jihar Ogun a makon jiya.

KU KARANTA: Osinbajo ya ce ana aiki ta yadda ziyartar yanar gizo zai kara sauki

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Wata Jiha a Najeriya Ya Rasu

Masanin shari’a ya ce an saba dokar National Health Act, 2014

A cewar wannan Lauyan, shugaban kasar a matsayinsa na mai rike da mukamin gwamnati, ya saba sashe na 46 na dokar lafiya watau National Health Act, 2014.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barista Enisenyin ya na so kotu ta yanke hukunci cewa zuwa ganin likita da mai girma shugaba Muhammadu Buhari yake yawan yi, ya ci karo da dokokin Najeriya.

Sannan Lauyan ya na so Alkali ya haramta fita da Muhammadu Buhari ya rika yi a baya da jirgin fadar shugaban kasa, har aka ajiye jirgin a filin saukar jirage a Ingila.

Rokon da ke gaban Alkalin kotun tarayya na garin Abeokuta

A dalilin wannan ne ake so kotu ta dakatar da gwamnatin tarayya daga cire kudi wajen daukar dawainiyar shugaba Muhammadu Buhari zuwa Landan a Ingila.

KU KARANTA: Mun samu karin Gwamna a APC - Hadimin Buhari

Kara karanta wannan

Cin Bashi Don Gudanar Ayyukan Cigaba Ba Laifi Bane: Cewar Bankin CBN

Lauya ya yi karar Buhari a kotu saboda yawan zuwa asibitocin waje da yake yi neman lafiya
Buhari a jirgin sama Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

The Nigeria Lawyer ta ce Enisenyin ya shigar da doguwar takardar korafi mai sakin layi 26 a gaban kotu, ya na tuhumar shugaban kasa da kuma Ministan shari’a.

Bayan babban lauyan gwamnatin tarayyar, Abubakar Malami, lauyan ya bukaci shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da majalisar tarayya su kare kansu.

Abin da dokar kasa ta ce

Lauyan ya ce dole sai Ministan lafiya da majalisar da ke kula da harkar kiwon lafiya ta amince kafin wani mai rike da kujerar gwamnati ya je ganin likita a ketare.

“Babu wani mai rike da mukami da za a dauki dawainiyar duba lafiyarsa ko jinyarsa a asibitin ketare face da amincewar majalisar da ke sa ido a kan harkar lafiya.”

Ministan lafiya ko kwamishinan lafiya (a jiha) ne zai amince da wannan dama da majalisar ta bada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng