Albishir: Gwamnatin Tarayya ta na kokarin ganin an koma sayen 1GB a kan N300 a Najeriya

Albishir: Gwamnatin Tarayya ta na kokarin ganin an koma sayen 1GB a kan N300 a Najeriya

  • Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya ce kudin ‘data’ zai ragu nan gaba
  • Nan da shekaru uku za a rika sayen 1GB a kan N390 inji Farfesa Yemi Osinbajo
  • Yemi Osinbajo ya yi wannan bayani ne wajen wani taro da aka gudanar a Abuja

Mataimakin shugaban kasa watau Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ta na kokarin ganin yadda za a kafa wani kamfani da zai karya farashin ‘data’.

Farfesa Yemi Osinbajo ya ce wannan kamfanin zai rika saida wa jama’an kasar nan kowane Gigabyte guda na damar hawa shafin yanar gizo a kan N390.

Daily Trust ta rahoto Mataimakin shugaban kasar ya na cewa ana sa ran za a cin ma wannan aiki nan da shekaru uku, zuwa lokacin gwamnati mai-ci ta shude.

KU KARANTA: Buhari ya fadawa MTN su rage kudin da su ke saida 'Data'

Farashin Data yau a kasuwa

Legit.ng ta fahimci cewa a halin yanzu mafi yawa kamfanonin sadarwan da su ke aiki a Najeriya, su na saida Gigabyte daya ne tsakanin N1,000 zuwa N1, 200.

‘Yan kasuwa da suke sarar ‘data’ daga kamfanoni su kan saida wa mutane a kan N300 zuwa N400. Hakan ya sa ake kukan farashin kasar nan ya yi tsada.

Nan gaba ‘Data’ zai yi araha sosai

Jaridar ta ce Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wannan albishir ne a wajen wani taro da kungiyar Nigerian Institution of Estate Surveyors and Valuers ta shirya.

Yemi Osinbajo ya ce zuwa lokacin da gwamnati ta kammala shimfida layin broadband a fadin kasar nan, farashin sayen ‘data’ zai fadi war-was, ya yi araha.

KU KARANTA: Kwamitin Majalisa na tuhumar Minista, NPA da yin bindiga da N166bn

Yemi Osinbajo
Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Bayan rage farashi da za ayi, mataimakin shugaban kasar ya ce za a samu cigaba da yadda za a iya sauke lodin megabyte 10 a cikin dakika guda a shafin yanar gizo.

Karamin Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Injiniya Abubakar Aliyu, ya wakilci Yemi Osinbajo a wajen wannan taro da aka yi ranar Alhamis, a birnin tarayya Abuja.

Wannan cigaba da za a kawo zai taimaka sosai, domin har yanzu ana fama da rashin sauri wajen bude shafuka saboda rashin karfin ‘data’ daga kamfanonin sadarwa.

A yau ne mu ka ji cewa Gwamnatin tarayya ta dauko aiki mai hadari, inda ta ke neman yadda za a kawo daidaito a tsarin biyan Ma’aikata, har an kai ga kafa kwamiti.

Shugaban ma'aikatar gwamnatin tarayya, Dr. Folasade Yemi-Esan ta kuma bayyana cewa sun kashe sama da Naira Biliyan biyu wajen biyan hakkin mamata a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel