Wata Sabuwa: Matsalar Tsaro ta Ta'azzara, An Umarci Bokaye Su Dauki Mataki

Wata Sabuwa: Matsalar Tsaro ta Ta'azzara, An Umarci Bokaye Su Dauki Mataki

  • Domin magance matsalar tsaro a wasu sassan kudancin Najeriya, gwamna ya ba bokaye umarnin daukar mataki
  • Gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya ce bokaye su nemo hanyar da za ta magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta
  • Ba wannan ne farko ba, tuni wata jihar Kudu maso gabas ta fara aiki da kambun tsafi domin magance matsalar tsaro

Gwamnatin jihar Oyo da ke kudancin Najeriya ta bai wa bokayen da ke jihar umarnin su dauki kowane irin mataki domin kawo karshen matsalar tsaro a jihar.

Legit.ng Hausa ta ruwaito ta BBC na cewa, kwamishinan Yada Labarai na jihar, Dr Wasiu Olatunbosun ne ya bayar da umarnin ga kungiyar masu maganin gargajiya ta jihar a madadin Gwamna Seyi Makinde na Oyo.

Ya tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta ba su dukkan goyon bayan da suke bukata domin taimakawa wajen samar da maganin matsalar tsaro.

KU KARANTA: Sojoji sun karyata Sheikh Gumi kan cewa jami'ansu na hada baki da 'yan bindiga

Wata Sabuwa: Matsalar Tsaro ta Ta'azzara, An Ba Bokaye Umarnin Magance Matsalar Tsaro
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa ta karade kowane yanki na Najeriya, ciki har da yankin kudu maso yamma inda kabilar Yarabawa ke da rinjaye mai yawa.

Hakazalika, yankin na fuskantar rikicin manoma da makiyaya kari a kan kungiyoyi masu fafutikar ballewa daga Najeriya da nufin kafa kasar Yarabawa ta Oduduwa.

An fara amfani da tsafi a kudu maso gabas don magance matsalar tsaro

Wani rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa an ajiye wani kambun tsafi a gaban babban ofishin 'yan sanda na jihar Abia da nufin kare hare-haren 'yan bindiga.

An gano cewa mazauna Bende road a Umuahia, babban birnin jihar, a ranar Talata 22 ga watan Yuni sun farka sun ga an ajiye kambun tsafin a inda aka takaita zirga-zirgan mutane da ababen hawa.

Duk da cewa a yanzu Legit.ng bata samu damar tabbatar da lamarin ba, rahoton da jaridar ta wallafa ya ambaci cewa mazauna unguwar sunyi ikirarin cewa an ajiye kambun tsafin ne don kare jami'an tsaro daga 'yan bindiga.

KU KARANTA: Bayan tura Burutai Benin, an tura tsoffin hafsoshin tsaro zuwa wasu kasashe

An Kwamushe Wani Sufeton ’Yan Sanda Dake Dillancin Makamai Da ’Yan Bindiga

A wani labarin, Wani Sufeton ‘yan sanda, Nathaniel Manasseh, ya shiga hannun 'yan sanda a Jihar Kuros Riba bisa zargin dillancin bindigogi da alburusai ga masu aikata laifuka.

An cafke Manasseh a Calabar, babban birnin jihar, kuma aka gabatar da shi a hedikwatar ‘yan sanda ranar Talata tare da sauran wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuka, an ce shi babban dillalin bindiga ne kuma ya dade yana wannan harkallar kafin dubunsa ya cika.

Sufeton da ya amsa laifin shi, an ce shi ne ke kula da ma'ajiyar makamai a rundunar 'yan sanda ta jihar kuma an kama shi ne lokacin da ya kasa ba da bahasin wasu kayan aiki ciki har da bindigogin AK-47 guda biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel