ISWAP: Sojojin sama da kasa sun yi taron-dangi, sun hallaka Mayakan Boko Haram rututu

ISWAP: Sojojin sama da kasa sun yi taron-dangi, sun hallaka Mayakan Boko Haram rututu

  • Sojoji sun tare mayakan Boko Haram suna shirin kai hari a garin Mainok
  • An yi amfani da jiragen yaki an bindige wasu motocin ‘Yan ta’addan ISWAP
  • Sojojin kasa sun taimakawa dakarun sama wajen wannan hari da aka kai

A wani hari na hadin-gwiwa da sojojin sama da na kasa suka kai a ranar Lahadi, 20 ga watan Yuni, 2021, an kashe ‘yan ta’addan Boko Haram da-dama.

Daily Trust ta fitar da rahoto a jiya cewa sojojin Najeriya sun kashe manyan sojojin da ‘yan kungiyar Islamic State for West Africa Province suke ji da su.

Yadda mu ka hallaka ‘Yan ISWAP - NAF

Mai magana da yawun bakin sojojin sama, Air Commodore Edward Gabkwet, ya shaida wa jaridar cewa sun duranma ‘yan ta’addan a hanyar zuwa Mainok.

KU KARANTA: An kashe 'Yan bindiga a Najeriya

‘Yan ta’addan na kungiyar ISWAP suna shirin shiga garin ne domin su yi ta’adi, kafin sojojin saman Najeriya suka auka masu da jiragen L-39 da MI-35.

“Mun samu labari ‘yan ta’adda sun yi gayya a motoci takwas, sun kama hanyar Mainok, babu wata-wata, muka tada jirage zuwa wurin.” Inji E. Gabkwet.

Air Commodore Edward Gabkwet ya ce jiragen yakin Alpha Jet na L-39 da MI-35 sun yi nasarar rugurguza shida daga cikin manyan motocin ‘yan ta’addan.

Babu labarin Modu Sulum

Rahoton ya ce sojojin ba su tabbatar da kisan sabon shugaban kungiyar ISWAP, Modu Sulum a harin da ya hallaka wasu manyan sojojin ‘yan ta’addan ba.

Boko Haram
Sojojin Boko Haram/ISWAP Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun hallaka wani Basarake a jihar Kaduna

Air Commodore Gabkwet ya ce: “Ba mu san wanene da wanene muka kashe ba a tagawar’yan ta’addan. Mun dai san mun yi nasarar ruguza motoci shida."

Rahotanni sun bayyana cewa Modu Sulum wanda a baya yake sana’ar saida ita ce, shi ne yake jagorantar ISWAP a yankin Allagarno, a karamar hukumar Kaga.

Kakakin rundunar ta NAF ya ce sojojin kasa sun taimaka a wannan hari. Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa yace ka da a bar ‘yan ta’addan su sarara.

A makon jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Borno, inda yi wa sojoji jawabi, ya bukaci su kara daura damara wajen yakar 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel