An sace tsohon ‘Dan Majalisa da wasu Bayin Allah yayin da ‘Yan bindiga suka dura Abuja

An sace tsohon ‘Dan Majalisa da wasu Bayin Allah yayin da ‘Yan bindiga suka dura Abuja

  • Wasu ‘Yan bindiga sun auka wani otel, sun yi gaba da mutane shida a Abuja
  • Har zuwa yanzu babu wanda ya ji labari game da halin da mutanen su ke ciki
  • Wannan lamari ya faru ne a yankin Tungan Maje, inda tun ba yau ba ana ta’adi

‘Yan bindiga sun shiga wai otel da ake kira Hilltop Hotel a unguwar Tunda Maje a babban birnin tarayya, sun dauke wasu mutane shida ranar Alhamis.

A ranar Alhamis, 24 ga watan Yuni, 2021, jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa an je wannan otel ne bayan gari ya yi duhu sosai, aka sace mutane.

‘Yan bindigan sun dauki kimanin mintuna 30 suna ta harbe-harbe ba tare da an iya yin komai ba, daga nan sai suka tasa keyar duk mutanen da suka kama.

KU KARANTA: Mutanen gari su tanaji N20m, mu na nan zuwa - 'Yan bindiga

An dauke tsohon ‘Dan majalisan jihar Kogi

The Guardian ta tabbatar da rahoton, ta ce daga cikin wanda aka dauke har da wani tsohon ‘dan majalisa daga jihar Kogi, Honarabul Sani Makama.

Sani Makama ya taba wakiltar mazabarsa a majalisar dokoki na jihar Kogi. Kwanan nan ya sauya sheka daga PDP, ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Babu tsaro a garin Tunga Maje

Rahotanni sun ce mazauna yankin Zuba sun shiga halin dar-dar a sakamakon abin da ya faru.

Unguwar Tunga Maje ta na cikin inda ake fama da matsalar rashin tsaro sosai a yankin birnin tarayya, an dade ana kawowa al’ummar yankin hari.

Jami'an tsaro
Jami'an tsaro Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Babu abin da ya hada Ali Modu Sheriff da Boko Haram - Kassim

Prince Frederick Adejoh wanda shi ne ya mallaki wannan otel, ya na cikin wadanda aka tafi da su. Adejoh ya na da sarautar Oma Onu Aya na kasar Igala.

Kamar yadda labari ya zo mana, kawo yanzu wadannan mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, ba su tuntubi iyalin wadanda suka dauka ba.

Kakakin ‘yan sanda ta Abuja, ASP ta tabbatar da wannan hari, ta ce rundunar ‘yan sanda suna kokarin ganin sun ceto mutanen ba tare da ko kwarzane ba.

A makon yau ne aka ji cewa shugaban kasa Muhammmadu Buhari ya amince a raba gidaje ga 'yan tawagar wasan Super Eagles da suka ci ƙasar AFCON 1994.

Mai girma Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a wani jawabi da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Alhamis a birnin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel