Yanzu-Yanzu: Sheikh Ahmad Gumi ya ƙaryata cewa DSS ta gayyace shi

Yanzu-Yanzu: Sheikh Ahmad Gumi ya ƙaryata cewa DSS ta gayyace shi

  • Babban malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya karyata cewa hukumar DSS ta gayyace shi
  • Sheikh Gumi ya ce yana tattaunawa da shugabannin hukumomin tsaro amma babu wanda ya gayyace shi
  • Fitaccen malamin mazaunin Kaduna ya ce wasu da ke neman janyo rudani ne suka kirkiri labarin amma babu gaskiya a cikin ta

Fitaccen malamin addinin musulunci, Dr Sheikh Ahmad Gumi ya ƙaryata cewa hukumar tsaron farar hula, DSS, ta gayyace shi, Daily Trust ta ruwaito.

Peter Afunanya, mai magana da yawun hukumar ya ce hukumar ta gayyaci malamin.

Yanzu-Yanzu: Sheikh Ahmad Gumi ya ƙaryata cewa DSS ta gayyace shi
Yanzu-Yanzu: Sheikh Ahmad Gumi ya ƙaryata cewa DSS ta gayyace shi
Asali: Original

DUBA WANNAN: Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

"DSS ta gayyaci Sheikh Gumi. Ba sabon abu bane hukumar ta gayyaci duk wani da ta ke son yi wa tambayoyi," ya shaidawa Daily Trust.

Amma a wani hira ta musamman da ya yi da Daily Trust, Gumi ya ce babu wanda ya gayyace shi.

Gumi ya shaidawa wakilin majiyar Legit.ng cewa wasu da suka ƙosa su ga an kama shi ne suka ƙirƙiri labarin.

Malamin addinin musuluncin ya ce duk lokacin da ya ke son shiga daji domin ya tattauna da yan bindiga, ya kan tuntubi jami'an tsaro, hakimai da wasu jami'an gwamnati kafin ya tafi.

KU KARANTA: 'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika

"Babu wanda ya gayyace ni. Kafafen watsa labarai ne ke son kawo rudani kuma da izinin Allah ba za su yi nasara ba. Muna tattaunawa da shugabannin hukumomin tsaro amma ba a gayyace ni ba," in ji shi.
Da aka masa tambaya ko ya ga rahoton cewa DSS ta gayyace shi, ya ce: "Eh, na karanta amma dariya kawai na yi. Na ce bari in kyalle su suyi farin ciki kan abin da suke tunanin rugujewa na ne amma karya ne, ba a gayyace ni ba."

VOA Hausa ta ruwaito cewa mai magana da yawun Gumi, Tukur Mamu, yana cewa an gayyaci Sheikh din zuwa ofishin DSS a Kaduna.

Kaduna: Yaya ya yi ƙarar ƙaninsa a kotun Shari'a saboda ƙin biyayya ga wasiyyar mahaifinsu da ya rasu

A wani labarin, kun ji wani mutum mai shekaru 40, Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.

Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.

Ya shaidawa kotu cewa mahaifinsu da Allah ya yi wa rasuwa ya bar wasiyya cewa a mayar da ɗaya daga ɗakunan gidan zuwa masallaci amma wadanda ya yi ƙarar sun saɓa umurnin mahaifin a cewar rahoton na Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel