Da Dumi-Dumi: Hukumar DSS ta gayyaci Gumi domin ya amsa tambayoyi

Da Dumi-Dumi: Hukumar DSS ta gayyaci Gumi domin ya amsa tambayoyi

  • Hukumar tsaron farar kaya ta DSS ta gayyaci Dr Sheikh Ahmad Gumi zuwa ofishinta
  • DSS ta gayyace Gumi ne kan zarginsa da furta kalaman da ta ce zagon kasa ne ga yaki da abokan gaba
  • Sai dai a bangarensa, Sheikh Gumi ya ce an jirkita masa maganansa ne inda ya ce abin da ya ke nufi shine akwai baragurbi cikin jami'an tsaro

Hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, a ranar Alhamis ta gayyaci babban malamin addinin musulunci da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi domin ya amsa tambayoyi, VOA ta ruwaito.

A cewar rahoton na VOA, an gayyaci Gumi ne bayan kallaman da aka ce ya yi na cewa jami'an tsaro hada kai da yan bindiga don aikata laifuka.

Dr Sheikh Ahmad Gumi
Fitaccen malamin addinin musulunci, Dr Sheikh Ahmad Gumi. Hoto: News Wire NG
Asali: Facebook

Gumi ya yi wannan ikirarin a lokacin da aka yi hira da shi a ARISE TV a ranar Laraba.

DUBA WANNAN: 'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika

Sai dai rundunar sojojin ta Nigeria ba ta amince da zargin da malamin na Kaduna ya yi ba tana mai cewa sojoji na sadaukar da rayyukansu domin yaki da ta'addanci.

Sanarwar da rundunar sojoji ta fitar.

"Yana da kyau mu tunatar da kanmu cewa rundunar sojoji da ake zargi da hada kai da bata gari sune suka sayar da rayyukansu wurin ceto wadanda aka sace a makarantar sakandare ta gwamnati a Birnn Yauri daga hannun masu garkuwa.

"Duk da cewa rundunar sojoji ba za ta ce babu baragurbi a cikin ta ba, ya zama dole a bayyana cewa ba za ta amince da duk wani yunkuri na yi wa tsaro zagon kasa ba ko taimakawa bata gari daga jami'anta."

Martanin Sheikh Gumi kan zargin da rundunar soji ta yi masa

Da ya ke mayar da martani ta bakin kakakinsa Malam Tukur Mamu Sheikh Ahmad Gumi ya yi watsi da zargin da rundunar sojojin ta yi masa yana mai cewa abin da ke faruwa a yanzu abin takaici ne.

KU KARANTA: Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

Mamu ya ce babu inda Shiekh Gumi ya yi ikirarin cewa sojoji baki dayansu ne ke da hannu wurin taimakawa bata gari sai dai ba za a rasa tsiraru ba, abin da ko rundunar ta soji ta amince da hakan kuma mutane da dama sun sha fadin hakan.

Rahoton na VOA ya ce Gumi ya bukaci rundunar sojoji da gidan talabijin din da ta yi hira da shi da suka jirkita kalamansa da su janye maganar tare da bashi hakuri idan ba haka ba zai dauki mataki na shari'a.

A wani labarin, wani mutum mai shekaru 40, Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.

Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164