Bidiyon amarya da ango suna yi wa juna kallon tsana yayin liyafar bikinsu ya janyo maganganu

Bidiyon amarya da ango suna yi wa juna kallon tsana yayin liyafar bikinsu ya janyo maganganu

  • Wata amarya da angonta sun janyowa kansu maganganu da tambayoyi a kafar sada zumunta bayan bidiyon bikinsu ya bazu
  • Ma'auratan an ga suna ciyar da juna tare da shayar da juna yayin da suke nuna tsabar bakin cikinsu duk da ranar aurensu ce
  • Sau da yawa bikin aure yana kasancewa mai dadi kuma ma'aurata na nun zumudinsu yayin da ake bikinsu amma wannan daban ne

Wasu masoya biyu da suka angonce sun janyo maganganu a kafar sada zumunta kan yadda suka ciyar da juna tare da shayarwa yayin liyafar bikinsu.

A wani bidiyo da @gossipboyz1 suka wallafa a Instagram, an ga ma'auratan suna yi wa juna kallon tsana da hantara a ranar bikinsu a maimakon murmushi yayin ciyar da juna.

KU KARANTA: Buhari ya umarci Pantami, Malami da wasu ministoci 3 su tattauna da Twitter

Bidiyon amarya da ango suna yi wa juna kallon tsana yayin liyafar bikinsu ya janyo maganganu
Bidiyon amarya da ango suna yi wa juna kallon tsana yayin liyafar bikinsu ya janyo maganganu. Hoto daga @gossipboyz1
Asali: Instagram

KU KARANTA: Bayan majalisa ta tabbatar da shi, COAS Yahaya ya sanar da muhimmin albishir ga sojin Najeriya

An ji bakin dake wurin suna tsokaci yayin da ma'auratan ke nuna tsana ga junansu. Angon ne ya fara ciyar da amaryar da kek yayin da itama ta bashi.

Sun sake maimatawa da ruwa inda ya bata, itama amarya ta bashi dukkansu rai a bace.

Su waye wadannan ma'auratan?

Legit.ng ta kasa gano su waye ma'auratan nan saboda wanda ya wallafa bidiyon a Instagram bai bada wani karin bayani ba bayan tsokacin da ya saka karkashin bidiyon.

Kamar yadda aka saka a kasan bidiyon: "Kalla tashin hankali a ko ina."

Me jama'a ke cewa?

Ma'abota amfani da Instagram sun cika sashin tsokaci da abinda ke ransu.

@tessy_diamond ta ce: "Gidan sauro ne ta saka a kanta?"

@hideezbeautypro tsokaci tayi da cewa: "Wannan fuskar amaryar tawa ce?"

@irabor.faith rubutawa yayi: "Amma yanayin kek din yayi kyau, sai dai ban san abinda yasa suke bakin ciki ba"

@favour091 cewa tayi: "Me yasa basu murmushi ne?"

A wani labari na daban, jami'ar jihar Kaduna ta bada umarni ga tsoffin dalibai da kuma sabbi da su dawo karatun shekarar 2020/2021 a ranar 22 ga watan Yuni.

Makarantar ta ce dole ne iyayen sabbi da tsoffin dalibai su saka hannu kan wata takardar alkawari cewa 'ya'yansu zasu kasance nagari.

Rijistran makarantar, Samuel Manshop, ya bada wannan umarnin a wata takardar da ya fitar a ranar Talata a Kaduna, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng