Ganduje: Aikin Ta'addanci a Najeriya Ya Shiga Mataki Na Gaba 'Next Level'

Ganduje: Aikin Ta'addanci a Najeriya Ya Shiga Mataki Na Gaba 'Next Level'

  • Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, yace yanzun aikata laifi a Najeriya ya shiga mataki na gaba
  • Gwamnan yace ya zama wajibi dabarun yaƙi da aikata laifuka shima ya shiga mataki na gaba, idan ana son a yi nasara
  • Gwamnatin Kano ta gina ruga domim fulani makiyaya su yi amfani da ita wajen kiwon su

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, yace ya zama wajibi a sanya fasahar zamani a yaƙi da matsalar tsaro a Najeriya matuƙar ana son a yi nasara, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babbar Magana: Wani Fitaccen Malami Yace Haramun Ne Yin Amfani da Alamar Dariya a Facebook

"Tunda aikata laifi a Najeriya ya shiga mataki na gaba, dabarun magance shi ya kamata ya shiga mataki na gaba shima," Ganduje ya faɗa yayin da ya tarbi sufeta janar na ƙasa, IGP Usman Baba, a Kano.

Gwamna Ganduje na jihar Kano
Ganduje: Aikin Ta'addanci a Najeriya Ya Shiga Mataki Na Gaba 'Next Level' Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mun Sanya na'urorin ɗaukar bidiyo a wasu wurare, Ganduje

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta saka na'urar CCTV a wasu muhimman wurare a faɗin jihar Kano, domin kare rayukan al'ummar Kano da dukiyoyinsu.

Yace: "Mun sanya na'urar CCTV a wasu muhimman wurare a ƙwaryar birnin Kano, kuma muna da masu bibiya da lura da na'urorin."

Gwamnatin Kano ta samar da ruga ga fulani makiyaya

Gwamna Ganduje ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta samar da ruga a dajin Ɗansoshiya wanda ya haɗa iyaka da jihar Katsina.

A cewar gwamnan, makiyaya suna jin daɗin amfani da wurin, kuma zai yi matukar wahala yan bindiga su maida dajin kamar gidansu.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Sanatoci Zasu Bayyana Sunayen Ma'aikatu, Hukumomin da Suka Ɓatar da Ƙudin Gwamnati

Ya ƙara da cewa mun yi wurin ɗaujar horon sojoji a dajin Falgore, wanda ɗaya ne daga cikin dazukan da suka fi girma a Najeriya.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Wani Dagaci da Matarsa a Ibadan

Yan bindiga sun yi garkuwa da Dagacin ƙauyen Araro, Chief Tafa Apanpa, tare da matarsa a jihar Oyo, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Wani mazaunin ƙauyen ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: