Hotuna da darajar katafaren gidajen Jeff Bezos sun bayyana cewa bashi da tsara

Hotuna da darajar katafaren gidajen Jeff Bezos sun bayyana cewa bashi da tsara

Duk da makuden kudin da ya biya MacKenzie na rabuwar aurensu, dukiyar Jeff Bezos ta cigaba da habaka a kullum, sakamakon Amazon da sauran hannayen jarin da suka sa ya zama mai kudin duniya.

Bezos na kaunar gidajen alfarma kuma Legit.ng ta tattaro muku katafaren gidajen da yake dasu a fadin Amurka.

KU KARANTA: Imanin da nayi da matasan Najeriya har yanzu yana nan daram, Aisha Buhari

Hotuna da darajar katafaren gidajen Jeff Bezos sun bayyana cewa bashi da tsara
Hotuna da darajar katafaren gidajen Jeff Bezos sun bayyana cewa bashi da tsara. Hoto daga Realtor.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Lawan: Bayan saukar mulkin Buhari, akwai yuwuwar APC ta fuskanci kalubale

1. New York (Madison Square Park, 212 Fifth Avenue - $96 million)

A watan Afirilu, Jeff Bezos ya bada $16 miliyan domin siyan wani gida mai dakuna uku a hawa na 20 dake 212 fifth Ave, New york Post ta ruwaito.

Wannan ya siya ne bayan ya biya wata $80 miliyan na siyan hawa na 21, 22, 23 da 24.

Hotuna da darajar katafaren gidajen Jeff Bezos sun bayyana cewa bashi da tsara
Hotuna da darajar katafaren gidajen Jeff Bezos sun bayyana cewa bashi da tsara. Hoto daga nypost.com
Asali: UGC

2. Lincoln Square (25 Central Park West - $13 million)

Biloniyan dan kasuwan ya mallaki gidaje hudu masu darajar $17.5 miliyan a Century Condominum dake 25 Central Park West.

Hotuna da darajar katafaren gidajen Jeff Bezos sun bayyana cewa bashi da tsara
Hotuna da darajar katafaren gidajen Jeff Bezos sun bayyana cewa bashi da tsara. Hoto daga nypost.com
Asali: UGC

3. Washington DC (Textile Museum, 2320-2330 S Street, Kalorama - $23 million)

A 2016, Bezos ya biya $23 miliyan na wani tsohon masakar tarihi dake Washington. Ya gyara wurin $12 miliyan. An gina gidan tarihin ne a 1914.

4. Home across the street (2325 S Street NW - $5 million)

Kamar yadda Washingtonian suka ruwaito, shugaban Amazon ya siya wani gida mai girman kafa 4,800 a kan $5 miliyan a watan Janairun 2020.

Gida ne mai dakunan bacci hudu wanda aka gina a 1951. Yana da bandakuna biyar, dakin gyara biyu da sauran ababen more rayuwa.

5. Beverly Hills. (Harry Warner Estate, Sunset Boulevard - $165 million)

Bezos ya siya wani katafaren gida na wani furodusa David Geffen kan kudi $165 miliyan. Wasu daga cikin abubuwan da gidan ya kunsa sun hada da tafki, lambu, wurin gyaran jiki, bangaren wasanni da sauransu.

Hotuna da darajar katafaren gidajen Jeff Bezos sun bayyana cewa bashi da tsara
Hotuna da darajar katafaren gidajen Jeff Bezos sun bayyana cewa bashi da tsara. Hoto daga Realtor.com
Asali: UGC

Sauran katafaren gidajen biloniyan sun hada da:

6. Spanish-style mansion (N. Alpine Dr. $24.5 million (N10,058,965,000))

7. Contemporary home (N. Alpine Drive. $12.9 million (N5,296,353,000))

8. West Texas Corn Ranch (Culberson and Hudspeth counties) - An yi kiyasin cewa Bezos ya biya $50 miiliyan domin siyansa.

9. Median, Washington (Evergreen Point. kusa da Post Office. $10 million (N4,105,700,000))

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbaji ya ce yana da tabbacin cewa Najeriya zata cigaba da zama kai hade a matsayin kasa daya duk da masu son ganin rabuwarta.

Ya sanar da haka a ranar Litinin a Abuja yayin taron farko na matasan jam'iyyar APC, Channels TV ta ruwaito.

"A bangaren son kawo hargitsi da rabewar kai, zan iya cewa mun fi karfi idan muna tare kuma a ganin duk masu fatan ganin rabewar kasar nan, basu kyauta ba," Farfesa Osinbajo ya sanar da taron matasa da masu ruwa da tsaki na APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng