Bayan majalisa ta tabbatar da shi, COAS Yahaya ya sanar da muhimmin albishir ga sojin Najeriya

Bayan majalisa ta tabbatar da shi, COAS Yahaya ya sanar da muhimmin albishir ga sojin Najeriya

  • Sojojin Najeriya sun samu albishir mai dadi daga COAS Manjo Janar Farouk Yahaya a ranar Talata, 22 ga wata Yuni a Enugu
  • Wannan murnar da sojojin suka fada ta biyo bayan wasu manyan alkawurra da shugaban sojin kasan yayi musu
  • Wasu daga cikin alkawurran da COAS yayi musu ya hada da inganta walwalarsa, samar musu da makaman zamani don yakar ta'addanci

Enugu

Manjo Janar Farouk Yahaya, shugaban sojin kasa na Najeriya a ranar Talata, 22 ga watan Yuni, ya sha alwashin cewa mulkinsa zai baiwa walwalar sojoji fifiko da duk goyon bayan da suke bukata.

COAS Yahaya wanda ya kai ziyarar farko ga Div 82 na rundunar soji dake Abakpa a Enugu ranar Talata, yayi alkawarin samar da kayan aiki ga sojojin domin sauke nauyin dake kansu cikin sauki.

KU KARANTA: An gano inda mambobin IPOB ke samun horarwa da kuma makamai

Bayan majalisa ta tabbatar da shi, COAS Yahaya ya sanar da muhimmin albishir ga sojin Najeriya
Bayan majalisa ta tabbatar da shi, COAS Yahaya ya sanar da muhimmin albishir ga sojin Najeriya. Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

KU KARANTA: Imanin da nayi da matasan Najeriya har yanzu yana nan daram, Aisha Buhari

A don haka yayi kira ga sojojin da su cigaba da kokari tare da kasancewa masu da'a a yayin da suke magance matsalar tsaro da ta'addanci a dukkan sassan kasar nan.

Na shiga aikin soja shekaru 36 da suka gabata

A ranar Talata, 15 ga watan Yunin 2021, Yahaya ya sanar da kwamitin tsaro na majalisar wakilai cewa ya shiga aikin soja tun shekaru 36 da suka gabata.

A yayin jawabi lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar domin tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban rundunar sojin kasa, Yahaya dan asalin jihar Sokoto ya ce ya taho da gogewarsa na shekaru 36.

Yahaya dan aji na 37 a makarantar horar da hafsin sojoji dake Kaduna, ya tabbatar da cewa zai inganta alakarsa da sauran shugabannin sojin domin inganta tsaro.

A wani labari na daban, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce jam'iyyar APC za ta iya fuskantar kalubale bayan sauka mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023, sai dai idan an kai taimakon gaggawa.

Lawan ya bada wannan jan kunnen ne a daren Litinin a jawabin da yayi na rufe taron farko na matasan jam'iyyar APC wanda aka yi a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamar yadda yace, dole ne jam'iyyar ta fara shiri domin rike kyawawan ayyukan wannan mulkin ta yadda za ta tabbatar da cewa an mika mulki hannun matasan jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng