Kotu ta kwace kadarorin sanatan APC saboda yawan bashin da ake binsa

Kotu ta kwace kadarorin sanatan APC saboda yawan bashin da ake binsa

  • Hukumar Kula da Kadarori ta Najeriya ta karbe kadarorin sanatan jam'iyyar APC mai ci
  • Kotu ta yanke hukuncin kwace kadarorin ne bisa kin biyan bashin da sanatan ya yi na banki
  • Rahoto ya ce, an ba da umarnin binciko kadarorin don tabbatar da sun bar hannun sanatan

Hukumar Kula da Kadarori ta Najeriya ta ce ta karbe kadarori mallakar dan majalisar Oyo ta Arewa, Sanata Abdulfatai Buhari, kan bashin N600m da kamfaninsa, Abadat Ventures Limited ya karba, Ripples Nigeria ta ruwaito.

AMCON a cikin wata sanarwa ta bakin kakakin ta, Mista Jude Nwauzor, ta ce Sanata Buhari ya karbo rancen ne daga Bankin Guaranty Trust kuma ya ki biya duk da tunatarwa da aka sha yi masa.

A cewar kamfanin, yanke hukuncin kwace kadarorin Sanata Buhari ya biyo bayan umarnin Mai Shari’a I. E Ekwo na Babban Kotun Tarayya, Abuja.

KU KARANTA: Duk wanda bai nuna shaidar ya yi NYSC ba kada a dauke shi aiki, DG ya ja kunne

Kotu ta kwace kadadrorin sanatan APC saboda yawan bashin da ake binsa
Sanata daga jihar Kwara, Abdulfatai Buhari | Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Wasu kadarorin da AMCON ta kwace sun hada da: kadarori a 12, St, Petersburg Street, Wuse II, Abuja da Plot 516 off Misau Crescent, off Birnin Kebbi Crescent, Garki II, Abuja.

Wani yankin sanarwar ya ce:

“Bisa bin umarnin Mai Shari’a I. E Ekwo na Babban Kotun Tarayya, Abuja, AMCON ta karbe kadarori mallakin Alhaji Buhari Abdulfatai, Babban Mai tallata kamfanin Abadat Ventures Limited kan bashin kusan N600m.
“Wani abin sha’awa shi ne, Alhaji Buhari Abdulfatai sanata ne na Tarayyar Najeriya mai wakiltar mazabar Ogbomosho ta Arewa a Jihar Oyo kan kujerar da ya ci a karkashin jam’iyyar APC mai ci.

Baya ga mallakawa AMCON kadarorin, kotun ta kuma umarci a dauki dukkan matakan da suka wajaba don sanin kadarorin, da nufin biyan bashin daidai da sashi na 553 da 554 na Dokar Kamfanoni da Kawance, 2020, Punch ta tattaro.

KU KARANTA: Cikakken Bayani: Da Ma Ginin Majalisar Dokoki ta Kasa Na Bukatar Gyara, Lawan https://hausa.legit.ng/1421758-da-dumi-dumi-ginin-majalisar-dokoki-ta-kasa-ya-wuce-lokacin-gyara-in-ji-lawan.html

Majalisa za ta binciki gwamnatin Buhari kan shirin farfado da tattalin arziki

A wani labarin, Majalisar dattijai a ranar Talata ta tambayi kwamitocinta a kan Tsarin Kasa; Banki, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi.

Ciki har da na Sufurin Ruwa; Sufurin Kasa da Ayyuka da Wuta don tattaunawa tare da Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Ahmed, kan shirin Farfado da Tattalin Arzikin Gwamnatin Tarayya na 2017 zuwa 2020, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan ya biyo bayan wani yunkuri ne "kan bukatar tantance tasiri kan ayyukan Tattalin Arziki da Ci Gaban Kasa (ERGP) na 2017 zuwa 2020" wanda Sanata Abdu Suleiman Kwari ya dauki gabatarwa majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.