Garba Shehu ya ce Buhari ne tauraron damokaradiyyar Najeriya

Garba Shehu ya ce Buhari ne tauraron damokaradiyyar Najeriya

  • Magoya baya, mabiya da masoyan shugaban kasa Muhammadu Buhari basu gazawa a wurin goyon bayansa
  • A cikin shekarun da suka gabata, wadanda ke bayan shugaban kasan har yanzu suna nan babu gudu babu ja da baya
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya ce masoyan shugaban kasan na cigaba da jin dadin nagartattun halinsa

FCT, Abuja

Babban mataimakin shugaban kasa Buhari a fannin yada labarai, Mallam Garba Shehu ya kwatanta shugaban kasa Muhammadu Buhari da tauraron damokaradiyya a Najeriya.

Shehu ya yi wannan tsokacin a ranar Talata, 22 ga watan Yuni yayin jawabi a wani kaddamar da littafi wanda wakilin Legit.ng ya halarta a Abuja.

KU KARANTA: Bidiyon 'yan sanda suna gudun ceton rai bayan jin sauti daga makabarta

Garba Shehu ya ce Buhari ne tauraron damokaradiyyar Najeriya
Garba Shehu ya ce Buhari ne tauraron damokaradiyyar Najeriya. Hoto daga Aso Rock
Asali: Facebook

KU KARANTA: Buhari ya umarci Pantami, Malami da wasu ministoci 3 su tattauna da Twitter

Littafi kan ayyukan Buhari

Mai magana da yawun shugaban kasa ya kwatanta littafin da cewa shugaban kasa Buhari aka kwatanta a dunkule, inda ya kara da cewa mawallafin, Abdullahi Haruna yayi aiki tukuru inda ya saukakawa masu magana da yawun shugaban kasan ayyukansu da abinda littafin ya kunsa.

A kalamansa: "Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne tauraron damokaradiyyar Najeriya. shugaban kasa Buhari mutum ne da mutane ke bi saboda suna kaunarsa sakamakon nagartarsa.

"Yana da halayya masu kyau kuma yana dauke da hali nagari wanda babu shugaba a Najeriya dake da shi. Ba zan sanar daku wadannan nagartar ba saboda abinda yanzu kuke da bukata shine karanta littafin nan.

"Zai baku labarin wannan shugaban gwarzo, mai gaskiya da rikon amana. Shugaban kasa ne da bai damu da kyale-kyalen rayuwa ba kuma hankalinsa yafi karkata ga 'yan kasa, talakawa da marasa karfi.

“Mutane zasu sha mamaki da abinda wannan littafin ya kunsa idan suka karanta saboda zai sanar dasu waye shugaban kasarsu. Wannan littafin ya bayyana waye Buhari kamar yadda masu magana da yawunsa suke bayyanawa, hakan ya zama mana tamkar saukaka aikinmu ne."

A wani labari na daban, Manjo Janar Farouk Yahaya, shugaban sojin kasa na Najeriya a ranar Talata, 22 ga watan Yuni, ya sha alwashin cewa mulkinsa zai baiwa walwalar sojoji fifiko da duk goyon bayan da suke bukata.

COAS Yahaya wanda ya kai ziyarar farko ga Div 82 na rundunar soji dake Abakpa a Enugu ranar Talata, yayi alkawarin samar da kayan aiki ga sojojin domin sauke nauyin dake kansu cikin sauki.

A don haka yayi kira ga sojojin da su cigaba da kokari tare da kasancewa masu da'a a yayin da suke magance matsalar tsaro da ta'addanci a dukkan sassan kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel