Buhari ya umarci Pantami, Malami da wasu ministoci 3 su tattauna da Twitter

Buhari ya umarci Pantami, Malami da wasu ministoci 3 su tattauna da Twitter

  • Shugaba Buhari ya umarci wasu ministoci biyar na Najeriya da su tattauna da Twitter
  • Kamar yadda Lai Mohammed ya sanar, gwamnatin tarayya ce ta kafa kungiyar ministocin
  • Gwamnatin tarayya ta dakatar da Twitter a Najeriya tun bayan da ta zargeta da katsalandan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje, Abubakar Malami, Antoni janar na tarayya da su tattauna da Twitter kan dakatar da ita da aka yi a Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta haramta Twitter a Najeriya tun bayan zargin kafar sada zumuntar da aka yi da katsalandan, Daily Trust ta wallafa.

Duk da matsantawa da aka yi daga kasashen ketare da kungiyoyi, gwamnatin Buhari ta cigaba da tsayuwa kan matsayarta.

KU KARANTA: Uwa ta gwangwaje danta da mota BMW yayin cikarsa shekaru 10 a duniya

Buhari ya umarci Pantami, Malami da wasu ministoci 3 su tattauna da Twitter
Buhari ya umarci Pantami, Malami da wasu ministoci 3 su tattauna da Twitter. Hoto daga dailytrust.com, Channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnan Neja ya dawo gida Najeriya, ya gana da iyayen daliban Tegina da aka sace

Amma a wata takarda da aka fitar a ranar Talata, Lai Mohammed, minsitan yada labarai, ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ta kafa kungiyar wadanda zasu tattauna da Twitter, Daily Trust ta ruwaito.

Baya da Fashola da Malami, sauran ministocin da zasu tatttauna da Twitter sun hada da Isa Pantami, ministan sadarwa, Chris Ngige, ministan kwadago da kuma Geoffrey Onyeama, ministan harkokin waje.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa kungiyar gwamnatin tarayya da zata tattauna da Twitter kan dakatar da ita da aka yi a Najeriya.

“Kungiyar ta gwamnatin tarayyan ta hada da Antoni Janar na tarayya kuma mai girma ministan shari'a, ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, minsitan harkokin waje, ministan gidaje da ayyuka da kuma ministan kwadago tare da sauran cibiyoyin gwamnati masu alaka.

Bayan dakatar da Twitter saboda ayyukanta da zasu iya zama barazana ga Najeriya, Twitter ta rubuto wasika ga shugaban kasa Buhari inda take bukatar gwamnatin tarayya ta sake bata dama," Mohammed ya sanar a wata takarda da Segun Adeyemi, mai magana da yawunsa ya fitar a madadinsa.

A wani labari na daban, mambobin kungiyar IPOB suna da wata yarjejeniya tsakaninsu da masu rajin raba kasar Kamaru a wasu fannoni na horarwa da kuma musayar makamai, Daily Trust ta tabbatar da hakan daga wata majiyar tsaro mai karfi.

Duk da har yanzu yanayin hadin kansu bai fito fili ba, bincike ya nuna cewa wani bangare na kasar Kamaru masu yaren Turanci kuma inda masu son kafa kasa Ambazonia suke suna iya shigowa Najeriya hankali kwance ta jihar Cross River wadanda suke da al'adu masu kamanni.

A yayin da IPOB ke yakar hukumomin tsaron Najeriya domin kafa jamhuriyar Biafra, masu neman yancin kai na Ambazonia suna bukatar a raba kasar Kamaru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel