Bidiyon 'yan sanda suna gudun ceton rai bayan jin sauti daga makabarta

Bidiyon 'yan sanda suna gudun ceton rai bayan jin sauti daga makabarta

  • Wani bidiyon mai cike da bada dariya na yadda 'yan sanda ke duba wani sauti da suka ji daga makabarta ya karade kafafen sada zumunta
  • A bidiyon, an ga 'yan sanda dauke da bindigogi da tociloli sun bayyana suna tafiya zuwa makabartar inda aka ce ana jin sauti
  • Amma kwatsam sai ga 'yan sandan na gudun ceton rai kamar yadda wani ma'abocin amfani da kafar Facebook ya wallafa

'Yan sanda basu da jarumtar da jama'a ke tsammani. Wani bidiyo da aka wallafa cikin kwanakin nan a kafar sada zumunta inda 'yan sanda biyu suka rude tare da firgita ya janyo cece-kuce.

A bidiyon, an ga wasu 'yan sanda tafe zuwa wata makabartar da aka yi korafin cewa ana samun sautika. 'Yan sandan dake dauke da bindigogi da tociloli an ga sun fara kwasar tseren ceton rai bayan sun ji sautin daga makabartar.

KU KARANTA: Gwamnan Neja ya dawo gida Najeriya, ya gana da iyayen daliban Tegina da aka sace

Bidiyon 'yan sanda suna gudun ceton rai bayan jin sauti daga makabarta
Bidiyon 'yan sanda suna gudun ceton rai bayan jin sauti daga makabarta. Hoto daga Traci Fant
Asali: Facebook

KU KARANTA: Mai siyar da motoci yayi wa Dino Melaye fallasa yace yana bin shi N14.5m tun 2019

Ga bidiyon yadda lamarin ya faru:

Jama'a sun yi martani

Bidiyon ya kasance wata hanyar nishadi ga dubban jama'a a kafar sada zumunta ta Facebook inda aka dinga dariya.

Jama'a da yawa sun kira 'yan sandan da sunaye daban-daban. Wasu sun ce a hakan ne zasu dinga hidimtawa jama'a tare da basu kariya?

Ga wasu daga cikin tsokacin jama'a:

Toot BossUp Goodine cewa yayi: "Na mutu! Ba zan iya amincewa da cewa zasu bani kariya kuma su hidimta min ba."

Helena Scrabblequeen McDaniel tace: "Kamar yadda 'yan sanda suka saba cewa idan an tare su 'Ina tsoron rasa rayuwata.'"

Rita Hunta ta ce: "Meye wannan? Basu je sun duba din ba!"

Christy Ramsey cewa tayi: "Ni kaina zan iya kamar hakan."

A wani labari na daban, mambobin kungiyar IPOB suna da wata yarjejeniya tsakaninsu da masu rajin raba kasar Kamaru a wasu fannoni na horarwa da kuma musayar makamai, Daily Trust ta tabbatar da hakan daga wata majiyar tsaro mai karfi.

Duk da har yanzu yanayin hadin kansu bai fito fili ba, bincike ya nuna cewa wani bangare na kasar Kamaru masu yaren Turanci kuma inda masu son kafa kasa Ambazonia suke suna iya shigowa Najeriya hankali kwance ta jihar Cross River wadanda suke da al'adu masu kamanni.

A yayin da IPOB ke yakar hukumomin tsaron Najeriya domin kafa jamhuriyar Biafra, masu neman yancin kai na Ambazonia suna bukatar a raba kasar Kamaru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng