An gano inda mambobin IPOB ke samun horarwa da kuma makamai

An gano inda mambobin IPOB ke samun horarwa da kuma makamai

  • Mambobin IPOB sun kafa wata yarjejeniya da masu rajin raba kasar Kamaru domin samun kasar Ambazonia
  • A wani bidiyo na taron yanar gizo da aka yi tsakanin shugaban IPOB da na Ambazonia, an ji suna yarjejeniyar samun horarwa da makamai tsakaninsu
  • 'Yan Ambazonia suna shigowa Najeriya ta jihar Cross River domin samun abinci,maboyar mata, da sauran ababen bukata saboda kamanceceniyar al'adunsu

Mambobin kungiyar IPOB suna da wata yarjejeniya tsakaninsu da masu rajin raba kasar Kamaru a wasu fannoni na horarwa da kuma musayar makamai, Daily Trust ta tabbatar da hakan daga wata majiyar tsaro mai karfi.

Duk da har yanzu yanayin hadin kansu bai fito fili ba, bincike ya nuna cewa wani bangare na kasar Kamaru masu yaren Turanci kuma inda masu son kafa kasa Ambazonia suke suna iya shigowa Najeriya hankali kwance ta jihar Cross River wadanda suke da al'adu masu kamanni.

KU KARANTA: Luguden wuta: Dan sanda ya sheke mutum 5, 4 sun jigata sakamakon tatil da yayi da giya

An gano inda mambobin IPOB ke samun horarwa da kuma makamai
An gano inda mambobin IPOB ke samun horarwa da kuma makamai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A yayin da IPOB ke yakar hukumomin tsaron Najeriya domin kafa jamhuriyar Biafra, masu neman yancin kai na Ambazonia suna bukatar a raba kasar Kamaru.

Daily Trust ta gano cewa akwai alaka tsakanin kungiyoyin biyu na kasar Najeriya da na kasar Kamaru.

Wani bidiyon taron da aka yi tsakanin shugaban IPOB, Nnamdi Kanu da shugaban AWL, Dr Lucas Cho Ayaba ya nuna cewa suna shirin yin aiki tare.

Yarjejeiniyar IPOB da Ambozonia

A yayin taron da suka yi ta yanar gizo a watan Afirilu, dukkan shugabannin sun sha alwashin aiki tare domin tabbatar da cewa kasashen duniya sun hanzarta assasa basu 'yancinsu.

Sun zargi cewa jama'ar dake yankunan biyu an takura musu kuma an haramta musu cigaba, lamarin da yafi mulkin mallaka takaici.

Yadda kamanceceniyar al'adu da iyakokinsu ke taimakawa shige da fice

Jihar Cross River tana da iyakoki da kudu maso yammacin Kamaru kuma suna da al'adu masu kama.

'Yan Ambazonia suna shiga yankunan iyakokin Cross River domin samun abinci, ruwan sha, maboya, mata da sauransu.

KU KARANTA: 2023: Manyan matsaloli 7 dake barazanar hargitsa APC a jihar Kano

A wani labari na daban, Alhaji Yusuf Galami, dan takarar jam'iyyar APC a zaben maye gurbi da aka yi domin cike kujerar majalisar tarayya ta mazabar Gwaram a jihar Jigawa ya samu nasara.

Farfesa Ahmad Shehu, baturen zaben, bayan tattara kuri'u daga akwatuna 248 ya bayyana Galambi a matsayin mai rinjaye da kuri'a 29,372 a kan Kamilu Inuwa na jam'iyyar PDP da ya samu kuri'u 10,047.

"Bayan Galambi ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben maye gurbin, ya zama mai nasarar a zaben," Shehu ya sanar da hakan a ranar Lahadi a Gwaram kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng