Yanzu-Yanzu: Buhari ya umurci Pantami, Fashola da wasu ministoci su tattauna da Twitter
- Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci tawagar gwamnatin tarayya ta tattauna da kamfanin Twitter game da dakatarwar da aka masa a Nigeria
- Tunda farko, gwamnatin Nigeria ta dakatar da ayyukan kamfanin ne bisa zargin ana amfani da dandalin wurin raba kan yan kasa da tada rikici
- Kungiyoyi da dama sun yi ta kira ga gwamnatin Nigeria ta janye dakatarwar amma bata amsa su ba sai dai ta ce za ta tattauna da kamfanin idan za ta amince da dokokin Nigeria
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, Ministan Shari'a, Abubakar Malami su tattauna da kamfanin Twitter game da haramta ayyukan kamfanin a Nigeria, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnatin tarayyar Nigeria ta dakatar da Twitter ne kan zargin ana amfani da ita wurin raba kan yan kasa da karfafa masu neman tada rikici a kasar.
KU KARANTA: Da Duminsa: Masu zanga-zangar 'Buhari Must Go' sun banka wuta a hanyar zuwa filin tashin jirage na Abuja
Duk da matsin lamba daga kungiyoyin kare hakkin mutane da kasashen waje, gwamnatin Buhari ba ta janye dakatarwar ba.
Amma a cikin sanarwar da Lai Mohammed, Ministan Labarai ya fitar a ranar Talata, ya sanar cewa gwamnati ta shirya wata tawaga da za ta tattauna da Twitter.
Bayan Fashola, sauran ministocin da ke cikin tawagar sun hada da Isa Pantami, Ministan Sadarwar da tattalin arzikin zamani, Chris Ngige, Ministan Kwadago, da Geoffrey Onyeama, Ministan harkokin kasashen waje.
KU KARANTA: Sheikh Gumi ya faɗawa gwamnatin tarayya abin da za ta yi don hana satar ɗalibai a makarantu
"Bayan dakatar da ayyukan ta a Nigeria saboda wasu ayyuka da ka iya raba kan yan kasa, Twitter ta rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari wasikar neman a zauna a tattauna game da dakatar da ita da nufin janye dakatarwar," kamar yadda Segun Adeyemi, kakakin Ministan Labaran ya bayyana.
A halin yanzu gwamnatin tarayya ta umurci ma'aikatunta da hukumomi da saurankafafe watsa labarai su dakatar da shafinsu na Twitter
A wani labarin daban, Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya bayyana cewa kamfanin Twitter ya taka rawar bayan fage a kan babbar zanga-zangar #EndSARS da aka yi shekarar da ta gabata, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Ministan ya faɗi haka ne a wurin binciken dokar hana twitter da kwamitocin majalisar wakilai da suka haɗa da, kwamitin labarai, ICT da shari'a ke gudanarwa.
Mr. Muhammed ya ce: "Kamfanin twitter ya tara wa masu zanga-zangar #EndSARS kuɗi, kafin daga bisani a karkatar da su ta wata hanyar."
Asali: Legit.ng