Mai siyar da motoci yayi wa Dino Melaye fallasa yace yana bin shi N14.5m tun 2019

Mai siyar da motoci yayi wa Dino Melaye fallasa yace yana bin shi N14.5m tun 2019

  • Fitaccen dan siyasan Najeriya, Dino Melaye, a cikin kwanakin nan ya sha caccaka bayan wani yace yana bin shi bashi bayan ya wallafa hotunan Rolls Royce dinsa
  • Wani mai amfani da unique motors a Instagram ya kira sanatan inda ya ke rokonsa da ya biya shi bashin da suke bin sa na wata mota tun 2019
  • Unique Motors yayi bayanin cewa har yanzu Dino ya rike masa wurin N14.5 miliyan ta wata mota kira Mercedes Benz da ya siya

Fitaccen dan siyasan Najeriya, Dino Melaye yayi fice wurin kaunar manyan motocin alfarma da kuma kudin da ya narka duk don kawata garejinsa.

Amma kuma babu wanda ya taba tsammanin cewa akwai wanda zai yi wa tsohon sanatan fallasa kan bashi.

A cikin kwanakin nan ne wani dillalin motoci a Instagram mai suna Unique Motors, yayi kira ga tsohon sanatan tare da yin ikirarin cewa yana bin shi wasu kudi na motar da ya siya.

KU KARANTA: Zaben maye gurbi: APC ta lallasa PDP a mazabar Gwaram ta tarayya dake Jigawa

Mai siyar da motoci yayi wa Dino Melaye fallasa yace yana bin chi N14.5m tun 2019
Mai siyar da motoci yayi wa Dino Melaye fallasa yace yana bin chi N14.5m tun 2019. Hoto daga @unique.motors
Asali: Instagram

KU KARANTA: Hotunan COAS Farouk Yahaya ya ziyarci sojojin da suka samu rauni a Maiduguri

A wata wallafa da Unique Motors tayi a labarinta na Instagram, sun wallafa hoton Dino tsaye kusa da wata mota kirar Mercedes Benz SUV wacce tuni dan siyasan yasa lambarsa a jikinta, sun yi ikirarin cewa bai biya ragowar kudin motar ba tun 2019.

Kamar yadda Unique Motors suka wallafa, suna son kawai ya biya su ragowar kudin mota da ya dauka.

Jama'a sun yi martani

Wasu ma'abota amfani da kafar sada zumuntar sun yi kira ga tsohon sanatan kuma sun yi martani.

Corpersdiary_ng cewa yayi: " Kai kai! Ina fatan wannan zargin ya zama karya ko kuma mu fara yi wa sanatan ba'a."

_Ava.officiall cewa tayi: "Dalilin da yasa bana yadda da duk abinda na gani a Instagram. Duk karya ce."

Ogechukwukama cewa yayi: "Ku kai shi kotu mana kuma ku daina damunmu."

A wani labari na daban, sauran shekaru biyu zabe amma akwai manyan kalubale dake kokarin tarwatsa jam'iyyar APC a jihar Kano, babbar cibiyar kasuwancin arewa kuma jihar da jam'iyyar ke takama da kuri'unta.

Manyan matsalolin da suka samu zama a babbar cibiyar kasuwancin arewan zasu iya zama kalubale ga jam'iyyar a fadin Najeriya saboda yawan kuri'un da ake samu daga jihar.

Matsalolin sun fara bayyana ne a ranar Laraba biyo bayan sanarwar dakatarwa da aka yi wa dan majalisa mai wakiltar birnin Kano a majalisar wakilai, Sha'aban Ibrahim Sharada.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel