Hotunan COAS Farouk Yahaya ya ziyarci sojojin da suka samu rauni a Maiduguri

Hotunan COAS Farouk Yahaya ya ziyarci sojojin da suka samu rauni a Maiduguri

  • Manjo Janar Farouk Yahaya ya ziyarci sojojin Najeriya da suke kwance a asibiti a garin Maiduguri
  • Ya tabbatarwa dakarun cewa lafiyarsu da walwalarsu ce mafi amfani don haka za a basu fifiko
  • Kwamandan OHK ya tabbatarwa da COAS cewa suna tsananta kokari wurin tabbatar da karshen ta'addanci

Shugaban rundunar sojin kasan Najeriya, Manjo Janar Faruk Yahaya, ya ziyarci sojojin da suka samu raunika yayin yakar 'yan ta'adda kuma suke kwance a asibitin koyarwa na Maiduguri.

A wata takarda da aka fitar a Maiduguri ta hannun Kanal Ado Isa, mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar Operation Hadin Kai kuma ya wallafa a Facebook, ya ce COAS ya je Maiduguri domin ziyarar kwanaki hudu don duba aiki da jin dadin dakarun dake jihar.

KU KARANTA: Hotunan cikin katafaren gidajen Mark Zuckerberg masu darajar N131b

COAS Farouk Yahaya ya ziyarci sojojin da suka samu rauni a Maiduguri
COAS Farouk Yahaya ya ziyarci sojojin da suka samu rauni a Maiduguri. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke likita a Magama, jihar Neja

"A yayin ziyarar, ya tabbatarwa da dakarun cewa zasu samu kula sosai a bangaren lafiya tare da tallafi a yakin da suke da ta'addanci.

"A yayin da yake asibitin, COAS ya dauka lokacinsa wurin tattaunawa da sojojin tare da tabbatar musu da cewa lafiyarsu ce abinda yafi muhimmanci.

“Ya jaddada musu cewa kasar nan tana alfahari da kokarinsu tare da sadaukarwarsu wurin tabbatar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.

“Hakazalika, COAS ya ziyarci bangaren kanikawa da yadda suke gyara ababen hawa a garejin ta hanyar amfani da kayayyakin cikin gida.

"Ya jinjinawa jajircewar injiniyoyin ta yadda suke gyaran ababen amfanin sojojin fiye da tsammani," Isa yace.

Ya kara da cewa kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa yayi bayanin yanayin aikin ga COAS inda ya tabbatar masa da kokarin da suke na tabbatar da kawo karshen ta'addanci.

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce wanda zai gaje shi zai rufe gidaje tare da ragargajesu domin habaka jihar fiye da yadda yayi a jihar.

Ya ce wasu jama'a na kallonsa a mai rusau kuma sun kosa wa'adin mulkinsa ya kare, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan wanda ya sanar da hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidajen rediyo a ranar Alhamis, ya ce mazauna jihar yanzu suna jinjina masa a kan yadda mulkinsa ke gyara birane.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel