Shugaba Buhari zai tafi Ghana don halartan taron kolin ECOWAS yau

Shugaba Buhari zai tafi Ghana don halartan taron kolin ECOWAS yau

  • A yayin taron shugabannin ECOWAS din za su yi nazari kan batun fasalta kungiyar da samar da kudin bai daya tsakanin kasashen
  • A yayin taron za a kuma tattauna kan halin siyasar kasar Mali wacce aka dakatar daga kungiyar
  • Shugaba Buhari zai samu rakiyar manyan jami’an gwamnatinsa guda 9

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron kolin shugabannin kasashen yammacin Afirka, na kungiyar ECOWAS karo na 59 da za a yi ranar Asabar a Accra babban birnin, Ghana.

Wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaban Kasa ta fuskar yada labarai, Malam Garba Shehu ya sanya wa hannu a ranar Juma’ah ta ce Shugaban wanda zai bar Abuja a ranar Asabar din zai hadu da takwarorinsa na kungiyar ta ECOWAS a taron tsakiyar shekara da shugabannin kungiyar za su yi in ban da Shugaban Kasar Mali, wacce aka dakatar daga kungiyar a watannin baya.

Ana sa ran tsohon Shugaban Kasar Najeriya Goodluck Jonathan, wanda shi ne manzon kungiyar na musamman kuma mai shiga tsakani a Mali zai gabatar wa shugabannin rahotonsa game da ziyarar aikinsa na karshe da ya kai zuwa kasar Malin.

DUBA NAN: Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa: Bankin Duniya

Shugaba Buhari zai tafi Ghana don halartan taron kolin ECOWAS yau
Shugaba Buhari zai tafi Ghana don halartan taron kolin ECOWAS yau Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU KARANTA: Na gina gida da daukar nauyin ‘ya’yana 15 - Dattijon da ya shekara 51 yana sana'ar sayar da jarida

Shugabannin kasashen za su kuma karbi rahoton yadda za a fasalta tsarin kungiyar da ya hada da batun samar da kudin bai daya da kuma daftarin yin karba-karba tsakanin shugabannin wajen tsayar da dan takarar Shugabancin Tarayyar Afirka daga daga yankin domin fitar da dan takara guda.

Sannan za a fitar da sanarwar bayan taron kan ababuwan da shugabannin suka cimma wa.

Shugaba Buharin zai samu rakiyar Ministan harkokin waje Geoffrey Onyema, da karamin Ministan harkokin wajen, Zubairu Dada, da Ministan tsaro, Manjo Janal Bashir Magashi (Mai ritaya), da Ministan lafiya Dokta Osagie Ehanire, Ministar baitil mali da tsare-tsaren kasa Zainab Ahmed, da mai bai wa Shugaban shawara kan tsaron kasa, Manjo Janal Babagana Monguno (Mai ritaya), da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da Darakta Janal na hukumar leken asiri ta kasa (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar.

Ana sa ran Shugaban zai dawo gida Najeriya da zarar an kammala taron.

Buhari ya janyo hankalin shugabannin Afrika

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya ce dole ne kasashen Afirka ta Yamma da ke fama da rikice-rikice su hada karfi da karfe don ceto yankin daga ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP.

Shugaban ya yi magana ne a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja, yayin karbar sabon Wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na Yammacin Afirka da yankin Sahel (UNOWAS), Mista Mahamat Saleh Annadif, dan kasar Chadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

iiq_pixel