Masu magana da yawun Buhari su ne babbar matsalarsa - Gwamnonin PDP
- Gwamnonin PDP a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni, sun caccaki wasu mataimakan shugaban kasa, musamman Garba Shehu
- Gwamnonin babbar jam'iyyar adawar ta Najeriya a wata sanarwa sun zargi Shehu da fadin ra'ayin kansa kan al'amuran kasa maimakon na Shugaba Buhari
- Bugu da ƙari, gwamnonin sun yi iƙirarin cewa manyan matsalolin gwamnati mai ci sune masu magana da yawun shugaban kasar
Gwamnonin Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP sun ce masu magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ba sa nuna matsayar shugaban kasa.
Babban daraktan kungiyar gwamnonin PDP, Honourable C.I.D. Maduabum, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni, ya lura cewa wasu daga cikin hadiman shugaban kasar kan harkokin yada labarai basa fadin ra’ayinsa, rahoton Channels TV.
KU KARANTA KUMA: Sace daliban Kebbi: Mun gazawa yaranmu, Shehu Sani ya koka
Maduabum, a madadin gwamnonin, ya yi zargin cewa:
“Shakka babu cewa masu magana da yawun Shugaba Buhari su ne babban matsalarsa a matsayin shugaban kasa. Ba sa wakiltansa yadda ya kamata."
Ya kuma yi fatali da kalaman Garba Shehu kan fitar da kudaden shiga da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) tayi da kuma tsarin kasuwar musayar kudaden kasashen waje a Najeriya.
Maduabum ya yi wa Shehu raddi kan martanin da ya yi game da dakatar da Twitter a Najeriya, kayayyakin more rayuwa, da ma'adanai a duk fadin kasar, jaridar Independent ta kuma ruwaito.
Ya ci gaba da cewa:
"Ta yaya mai magana da yawun shugaban kasa zai zama kurma? Ya gaza ganin mummunar cin zarafin da aka yi wa 'yancin magana. Ba ya ganin bukatar karfafa gwiwar matasanmu. Yana wofantar da abubuwa masu mahimmanci na ƙasa. Abin takaici ne matuka."
Buhari ya fadi Gwamnonin da suka hana a ga karshen rikice-rikice
A wani labarin, fadar shugaban kasar Najeriya ta ce gwamnonin jam’iyyar PDP ba su ba gwamnatin tarayya gudumuwa wajen shawo kan rigimar makiyaya da manoma.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta kawo rahoto, Garba Shehu ya fitar da jawabi a ranar Laraba, ya na mai maida martani ga kungiyar gwamnonin jihohin PDP.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya yi raddi ga kalaman da gwamnonin su ka yi a ranar Litinin.
Asali: Legit.ng