'Yan hana ruwa gudu: Buhari ya fadi Gwamnonin da suka hana a ga karshen rikice-rikice

'Yan hana ruwa gudu: Buhari ya fadi Gwamnonin da suka hana a ga karshen rikice-rikice

  • Fadar Shugaban kasa ta yi tir da Gwamnonin jihohin hamayya na PDP a Najeriya
  • Garba Shehu ya ce Gwamnonin sun hana kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali
  • Gwamnonin PDP ba su bada gudumuwar yadda za a ci da kasa gaba inji Hadimin

Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce gwamnonin jam’iyyar PDP ba su ba gwamnatin tarayya gudumuwa wajen shawo kan rigimar makiyaya da manoma.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta kawo rahoto, Garba Shehu ya fitar da jawabi a ranar Laraba, ya na mai maida martani ga kungiyar gwamnonin jihohin PDP.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya yi raddi ga kalaman da gwamnonin su ka yi a ranar Litinin.

KU KARANTA: Buhari ya ba raba aiki ga wadanda aka kashe masu 'yanuwa a zaben 2011

Malam Garba Shehu yake cewa: “Dabarun da muka kawo za su kawo karshen kalubalen da kasar mu ta ke fuskanta, amma gwamnonin PDP sun ki karbar lamarin.”

“Da haka, gwamnonin PDP sun toyewa ‘yan Najeriya hakkinsu na zama, su nemi abinci a duk jihar da suka ga dama a tarayya, sun zabi kawo sabanin kabilanci.”

A jawabin na sa, Garba Shehu, ya zargi gwamnonin adawa da jawo kiyayya a tsakanin mutanen Najeriya, a madadin yin abin da zai jawo zaman lafiya a kasar nan.

Jaridar The Guardian ta ce hadimin shugaban kasar ya zargi jihohin adawa da kin kawo shawarar da za ta taimaki Najeriya yayin da ake fama da matsin tattali.

Mal. Garba Shehu
Shugaba Buhari da Garba Shehu Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

KU KARANTA: A sa doka game da yadda ake amfani da shafukan yanar gizo - FG

Haramta Twitter

Shehu ya soki matsayar gwamnonin PDP a kan haramta Twitter, ya na mai kare gwamnatin tarayya, ya ce matakin da aka dauka ya rage yaduwar labaran karya.

“Gwamnonin suna neman inda za su samu karin kudi, su na makokin rashin hawa kafofin yada labarai ta yadda za su yada labaran bogi da na kiyayya.” Inji Shehu.

Martanin Gwamnonin PDP

Gwamnonin da aka zaba a jam’iyyar PDP sun yi wa Garba Shehu raddi, su ka yi tir da jawabinsa, su ka ce kalamansa ba su yi kama da wanda shugaban kasa zai yi ba.

A baya an ji cewa Gwamnonin adawa na PDP sun hadu, za su yi zama na musamman a garin Uyo a makon nan a karkashin jagorancin gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Aminu Waziri Tambuwal ya caccaki gwamnatin Muhammadu Buhari, ya kuma ce za su karbe shugabancin kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel