Madubin dubawa a siyasa: Tsohuwar ministar kudi tana cikin alhini kwanaki 40 bayan rasuwar Mama Taraba

Madubin dubawa a siyasa: Tsohuwar ministar kudi tana cikin alhini kwanaki 40 bayan rasuwar Mama Taraba

  • Sanata Nenadi Esther Usman ta jinjina wa kawarta, marigayiya Sanata Aisha Jummai Alhassan
  • Tsohuwar ministar kudin ta bayyana tsohuwar ‘yar takarar gwamnan a matsayin madubin dubawa ga yara mata a fannin siyasa
  • Mama Taraba, kamar yadda aka fi saninta da shi, ta yi aiki a matsayin ministar harkokin mata a lokacin mulkin Shugaba Buhari na farko

Kwanaki arba'in bayan rasuwar Sanata Aisha Jummai Alhassan wacce aka fi sani da Maman Taraba, tsohuwar ministar kudi, Sanata Nenadi Esther Usman tana bakin cikin rasuwar ƙawarta har yanzu.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Nenadi wacce ta wakilci yankin Kudancin Kaduna a majalisar dattawa a cikin wata sanarwa ta ce mutuwar Alhassan ta raba kasar da ‘yar kishin kasa ta gaskiya.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa masu ban mamaki 4 game da Naira 100 na Najeriya da ba lallai ne ku iya sani ba

Madubin dubawa a siyasa: Tsohuwar ministar kudi tana cikin alhini kwanaki 40 bayan rasuwar Mama Taraba
Mama Taraba ta yi kwanaki 40 da rasuwa a ranar Laraba, 16 ga watan Yuni Hoto: @Eyecontact4MamaTaraba2019
Asali: Facebook

Nenadi da take magana a addu’an arba’in na marigayiyar da aka yi a ranar Laraba, 16 ga watan Yuni, a Kaduna ta ce har yanzu tana cikin rudu, in ji jaridar Leadership.

A cewar tsohuwar ministar, Alhassan ta kasance madubin duba ga yara mata a bangaren siyasa. Yayin da take jinjinawa marigayar yar takarar gwamnan, Nenadi ta lura cewa za a ci gaba da tunawa da Mama Taraba har abada a matsayin mace daya da ta yi magana da gaskiya ga mulki.

Ta yi addu'ar Allah ya gafarta mata kurakuranta ya kuma ba ta hutu na har abada.

KU KARANTA KUMA: Ibo ne manyan masu hannun jari a Najeriya, ba za mu fice ba - In ji Iwuanyanwu

Na Kaɗu Matuƙa Da Samun Labarin Mutuwar Aisha Alhassan, Atiku

A baya mun kawo cewa, tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya nuna alhini a kan mutuwar tsohuwar ministar harkokin mata, Aisha Alhassan Jummai.

Aisha wacce aka fi sani da suna Mama Taraba, ta rasu a ranar Juma’a, 7 ga watan Mayu, a Alkahira, Masar.

Atiku ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai tausayi da biyayya da burin ganin an samu Najeriya mai inganci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel