Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC ya sake galaba kan ɗan takarar PDP a kotun ɗaukaka ƙara a Ondo
- Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da Eyitayo Jegede ya shigar na kallubalantar nasarar Gwamna Rotimi Akeredolu a zaben gwamna
- A ranar Laraba 16 ga watan Yuni ne alkalan kotun daukaka kara da ke zamanta a Akure jihar Ondo suka yanke hukuncin
- Kotun ta jaddada nasarar Akeredolu tana mai cewa dan takarar na jam'iyyar PDP ba shi da wasu kwararran hujjoji
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Akure, babban birnin jihar Ondo ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna a jihar na Peoples Democratic Party, PDP, Mr Eyitayo Jegede ya shigar na kallubalantar nasarar Gwamna Rotimi Akeredolu wanda shine dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress, APC a zaben.
The Punch ta ruwaito cewa tunda farko kotun sauraren kararrakin zabe ta yi watsi da karar da dan takarar na PDP ya shigar na kallubalantar zaben saboda rashin kwararran hujojji amma Jegede ya daukaka kara a kotun na gaba.
DUBA WANNAN: Zanga-Zanga ta ɓarke gidan yari yayin da gandireba ya bindige wani baƙo har lahira
Premium Times ta ruwaito cewa kotun daukaka karar, bayan ta yi nazari kan dalilai bakwai da mai daukaka karar ya gabatar mata ta yi watsi da karar tana mai cewa ba shi da kwararran hujjoji.
KU KARANTA: An kama matar da ta damfari ɗan siyasa N2.6m da sunan za a yi amfani da 'iskokai' a taimaka masa ya ci zaɓe
Jagoran lauyoyin, Theresa Orji-Abadua ya ce karar da Mr Jegede ya shigar ba ta da nagarta.
Lauyan Mr Jegede, Onyeachi Ikpeazu ya shaidawa kotun daukaka karar cewa tsayarda Mr Akeredolu da jam'iyyar APC ta yi a matsayin dan takara ya saba wa doka.
Sai dai kotun ta ce wannan lamari ne na jam'iyya don haka kotunsa bata da hurumin cewa wani abu a kai. Lauyan Mr Akeredolu da hukumar zabe mai zaman kanta INEC suma sun amince da hakan.
A wani labarin, yan sanda a jihar Bayelsa sun kama wani Mr Akpoviri Vincent Jimmy wanda aka ce ya dade yana bi asibitoci dauke da lasisin likita yana neman aiki a matsayin mai tiyata a jihohin Delta da Bayelsa, Daily Trust ta ruwaito.
Linda Ikeji ta ruwaito cewa mai magana da yawun yan sandan jihar Bayelsa, Asinim Buswat ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa sunansa Dr Charles kuma yana aiki a jihar Taraba kafin a gano shi.
Asirin Jimmy ya fara tonuwa ne a Ughelli a jihar Delta a lokacin da ya kasa fadin wasu kalamai da ya dace kowanne kwararren likita ya sani.
Asali: Legit.ng