'Yan bindiga sun sheke mutum 1, sun yi garkuwa da 'yan Chaina 2 a Taraba

'Yan bindiga sun sheke mutum 1, sun yi garkuwa da 'yan Chaina 2 a Taraba

  • Miyagun 'yan bindiga a jihar Taraba sun sheke mutum daya tare da sace 'yan Chaina biyu
  • Lamarin ya faru a wani wurin hakar ma'adanai ne dake tsakanin jihohin Binuwai da Taraba
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, David Misal, ya tabbatar da aukuwar lamarin

'Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu 'yan kasar Chaina a jihar Taraba.

Lamarin ya faru a daren Litinin a wani wurin hakar ma'adanai a yankin Arufu dake karamar hukumar Wukari ta jihar Taraba.

David Misal, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Channels TV a wata hira ta wayar salula a ranar Laraba.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi: Dangote ya fahimci 'yan Najeriya fiye da yawancin 'yan siyasa

'Yan bindiga sun sheke mutum 1, sun yi garkuwa da 'yan Chaina 2 a Taraba
'Yan bindiga sun sheke mutum 1, sun yi garkuwa da 'yan Chaina 2 a Taraba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Bankin duniya ya karyata FG, ya ce 'yan Najeriya 7m suka fada talauci

Rundunar 'yan sanda ta bada tabbacin za ta shawo kan lamarin

Ya bada tabbacin cewa 'yan sandan na kan lamarin kuma tuni sun fara farautar 'yan bindigan yayin da ake cigaba da bincike.

Mai magana da yawun rundunar ya tabbatar da cewa 'yan kasar Chaina biyun da aka sace suna aiki ne da wani kamfanin hakar ma'adanai a jihar.

Ya kara da cewa wasu da yawa sun samu miyagun raunika yayin da suke gudun neman tsira kuma an mika su asibiti domin duba lafiyarsu.

Inda lamarin ya faru

Yankin yana tsakanin jihar Binuwai da Taraba kuma ya kasance a kanun labarai wurin hare-hare ballantana wuri ne da ake hakar ma'adanai.

Kamar yadda kakakin rundunar ya sanar, har yanzu ba a samu wayar wadanda aka sace ba balle miyagun su bukaci kudin fansa, Channels TV ta ruwaito.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci garin Maiduguri dake jihar Borno a ranar Alhamis na kwana daya, inji Gwamna Babagana Umara Zulum.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a yammacin ranar Talata a gidan gwamnatin jihar dake Maiduguri inda yace shugaban kasan zai duba yanayin halin da tsaron yankin arewa maso gabas yake ciki, Channels TV ta ruwaito.

A yayin ziyarar, ya ce shugaban kasan zai kaddamar da gidaje 4,000 wadanda suke daga cikin aikin gidaje na gwamnatin tarayya tare da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel