Gwamnan Bauchi: Dangote ya fahimci 'yan Najeriya fiye da yawancin 'yan siyasa

Gwamnan Bauchi: Dangote ya fahimci 'yan Najeriya fiye da yawancin 'yan siyasa

  • Bala Mohammed gwamnan jihar Bauchi ya ce Dangote ya fahimci 'yan Najeriya fiye da yawancin 'yan siyasa
  • Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin wata ziyara da jami'an gidauniyar Dangote suka kai masa a jiharsa
  • Kauran Bauchi ya roki Dangote da ya duba jiharsa kuma ya saka hannayen jari saboda akwai zaman lafiya

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote ya fi fahimtar 'yan Najeriya fiye da wasu 'yan siyasar kasar nan.

Mohammed ya sanar da hakan ne a Bauchi a ranar Talata yayin da jami'an gidauniyar Dangote suka ziyarcesa, TheCable ta ruwaito.

Gwamnan ya kwarzanta biloniyan dan kasuwan a kan yadda yake tallafawa mata da masu bukatar taimako a kasar nan.

Gwamna Bala Mohammed ya jinjinawa Dangote

"Ya bayyana jarumtarsa na mutumin da yayi nasara a fannin kasuwanci inda kuma yake taimakawa ga marasa karfi da kuma duk wanda ya samu damar tallafawa," Mohammed yace.

KU KARANTA: Tsoho mai shekaru 56 da kifi ya hadiye kuma ya amayo shi, ya bada labari dalla-dallaKU K

Gwamnan Bauchi: Dangote ya fahimci 'yan Najeriya fiye da yawancin 'yan siyasa
Gwamnan Bauchi: Dangote ya fahimci 'yan Najeriya fiye da yawancin 'yan siyasa. Hoto daga thecableng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Asari Dokubo: Abinda Fani-Kayode ya sanar da ni yayin da Nnamdi Kanu ya turo shi wurina

"Ba wai bangaren ilimi da lafiya kawai yake ginawa ba a fadin duniya, yana gangarawa har zuwa mabukata kuma yana samarwa mutane da yawa abinci.

"Daga abinda ya nuna, ya bayyana cewa ya fahimci Najeriya fiye da yawancin 'yan siyasa saboda shi ke tallafawa masu daukar dawainiyar iyalansu."

"Mun san yadda kamfanin Dangote yake da abubuwan da suke yi. Suna yin shi ne cikin tsari kuma a kimiyyance," yace.

Kauran bauchi ya roki Dangote ya zuba hannun jari a jiharsa

“Ina rokonku da ku zo ku duba abinda muke da shi a nan. Akwai zaman lafiya a Bauchi kuma hannayen jarinku zasu samu kariya saboda yana daga cikin jihohi masu zaman lafiya a arewacin Najeriya."

Gwamnan ya roki kamfanin Dangote da ya je jihar Bauchi ya saka hannun jari saboda jihar tana daga cikin jihohi masu zaman lafiya a Najeriya, The Cable ta ruwaito.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya a ranar Talata ta tabbatar da cewa Twitter ta rubuto mata wasika da bukatar tattaunawa kan matsalolin da suka sa gwamnatin ta dakatar da ita.

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya tabbatar da hakan yayin da ya bayyana a shirin "siyasar kasa baki daya", wani shirin gidan rediyon Najeriya ne da Kamfanin Dillancin Labarai ya kiyaye a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

"Ina tabbatar muku da cewa Twitter ta yi wa gwamnatin tarayya wasika na cewa ta shirya tattaunawa. Kamar yadda muka ce, kofa a bude take amma sai Twitter ta yi abinda ya dace," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel