Bankin duniya ya karyata FG, ya ce 'yan Najeriya 7m suka fada talauci

Bankin duniya ya karyata FG, ya ce 'yan Najeriya 7m suka fada talauci

  • Bankin duniya ya karyata gwamnatin tarayya a kan ikirarin Buhari na cewa gwamnatinsa ya fitar da 'yan Najeriya miliyan 10 daga fatara
  • Kamar yadda bankin duniyan ya tabbatar, sabbin mutum miliyan bakwai ne suka sake tsundumawa talauci a Najeriya
  • Sai dai an sha mamakin wannan kiyasin ganin cewa NBS ta tabbatar da saukar farashin kayan abinci a watan Mayun da ya gabata

Kasa da kwanaki uku bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa mulkinsa ya tsamo mutum miliyan 10 daga talauci, bankin duniya ya ce tashin farashin kayan abinci ya tsoma mutane miliyan bakwai cikin fatara, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan ikirarin na shugaban kasan da na bankin duniyan ya zo ne a yayin da hukumar kididdiga ta kasa ta ce hauhawar farashin kayan abinci ya sauka da kashi 0.19 a watan Mayun 2021 yayin da kuma 'yan Najeriya ke ta kokawa kan hauhawar ababen bukata na rayuwa kamar abinci, magunguna da sauransu.

KU KARANTA: Twitter ta rubutowa FG wasika, tana bukatar a tattauna kan dakatar da ita

Bankin duniya ya karyata FG, ya ce 'yan Najeriya 7m suka fada talauci
Bankin duniya ya karyata FG, ya ce 'yan Najeriya 7m suka fada talauci. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Faruk Yahaya: Ina da gogewa a fannin yaki, zan iya shawo kan matsalar tsaron Najeriya

Kwarraru sun ce hukuncin bankin duniyan ya zo a ba-zata ganin cewa hatta NBS wacce ita ce hukumar kididdiga ta kasa a watannin da ya gabata sun tabbatar da cewa hawan farashin kayan abinci ne ya ke kawo tashin sauran kayayyaki.

A wata takarda da aka fitar a Abuja a ranar talata, bankin duniya ya ce: "Farashin kayan abinci shi ke kawo tashin farashin kayayyaki. Tashin farashin kayayyakin kuwa shi ya jefa 'yan Najeriya miliyan bakwai a fatara a 2020 kadai."

Takardar da ta samu saka hannun mai magana da yawun bankin, Mansir Nasir, ta ce yayin da gwamnati ta dauka matakan baiwa tattalin arzikin kasar nan kariya, ya dace a kafa sabuwar doka da zata kawo farfadowarsa.

Kiyasin wanda aka yi dogaro da binciken shekarar da ta gabata, ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya ya sake kasa da kashi -1.8 ba kamar yadda aka kintata ba na -3.2 a 2020 duba da annobar korona, Daily Trust ta ruwaito.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote ya fi fahimtar 'yan Najeriya fiye da wasu 'yan siyasar kasar nan.

Mohammed ya sanar da hakan ne a Bauchi a ranar Talata yayin da jami'an gidauniyar Dangote suka ziyarcesa, TheCable ta ruwaito.

Gwamnan ya kwarzanta biloniyan dan kasuwan a kan yadda yake tallafawa mata da masu bukatar taimako a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng