'Yan bindiga sun kurmushe gidan dan majalisa a Imo, sun sheke maigadi

'Yan bindiga sun kurmushe gidan dan majalisa a Imo, sun sheke maigadi

  • Hankalin jama'a ya tashi a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo bayan 'yan bindiga sun kai farmaki
  • Sun kai mugun harin ne gidan dan majalisa Ekene Nnodumele inda suka kone gidan kurmus
  • Ndumele ya tabbatar da kone gidansa da aka yi tare da sheke maigadinsa da suka yi har lahira

Tashin hankali da rashin natsuwa ya sauka a Ebenator dake Awo Omama a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo bayan 'yan bindiga sun kai farmaki garinsu dan majalisa mai wakiltar mazabar Orsu a majalisar jihar Imo, Ekene Nnodumele a ranar Laraba.

An gano cewa 'yan bindigan sun cire kan maigadi dake aiki kafin su bankawa gidan wuta, Daily Trust ta ruwaito.

Manema labarai sun tattaro cewa 'yan bindigan sun kone gidan tsohon antoni janar da kwamishinan shari'a, Cyprain Charles Akaolisa a yankin.

KU KARANTA: Ahmed Musa yayi martani mai zafi bayan sun sha da kyar a filin wasa a Kaduna

'Yan bindiga sun kurmushe gidan dan majalisa a Imo, sun sheke maigadi
'Yan bindiga sun kurmushe gidan dan majalisa a Imo, sun sheke maigadi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi: Dangote ya fahimci 'yan Najeriya fiye da yawancin 'yan siyasa

Dan majalisar ya tabbatar da aukuwar lamarin

Ndumele wanda ya tabbatar da farmakin da aka kai gidansa, ya kwatanta lamarin da abun mamaki, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce bai taba tsammani ba saboda bashi da wata matsala da kowa da har zai sa a kai masa wannan farmakin.

Ya tabbatar da tsinke kan tare da kashe maigadin gidansa da aka yi.

Ya ce, "Ban taba tsammanin haka ba saboda bani da hayaniya ko wata matsala da kowa. Ina aiki kuma ina wakiltar jama'ar Orsu da kyau. Jama'armu basu da matsala kuma ina da tabbaci sojan haya aka sa. Kisan kai ba halin mutanen Orsu bane domin baya cikin al'adarmu."

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci garin Maiduguri dake jihar Borno a ranar Alhamis na kwana daya, inji Gwamna Babagana Umara Zulum.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a yammacin ranar Talata a gidan gwamnatin jihar dake Maiduguri inda yace shugaban kasan zai duba yanayin halin da tsaron yankin arewa maso gabas yake ciki, Channels TV ta ruwaito.

A yayin ziyarar, ya ce shugaban kasan zai kaddamar da gidaje 4,000 wadanda suke daga cikin aikin gidaje na gwamnatin tarayya tare da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: