Wani mutum da ke ƙaryar cewa shi likita ne mai tiyata ya shiga hannu a Bayelsa

Wani mutum da ke ƙaryar cewa shi likita ne mai tiyata ya shiga hannu a Bayelsa

  • Rundunar Yan sanda a jihar Bayelsa ta ce ta kama wani mutum da ke ikirarin cewa shi likita ne
  • An fara zargin cewa shi ba likita bane a lokacin da ake masa tambayoyi kafin daukansa aiki
  • Akpoviri Vincent Jimmy ya amsa cewa shi ba likita bane kuma ya sace takardun abokinsa ne ba tare da saninsa ba

Yan sanda a jihar Bayelsa sun kama wani Mr Akpoviri Vincent Jimmy wanda aka ce ya dade yana bi asibitoci dauke da lasisin likita yana neman aiki a matsayin mai tiyata a jihohin Delta da Bayelsa, Daily Trust ta ruwaito.

Linda Ikeji ta ruwaito cewa mai magana da yawun yan sandan jihar Bayelsa, Asinim Buswat ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa sunansa Dr Charles kuma yana aiki a jihar Taraba kafin a gano shi.

Akpoviri Vincent Jimmy
Wanda ake zargi da karyar likitanci, Akpoviri Vincent Jimmy. Hoto: Linda Ikeji
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Zanga-Zanga ta ɓarke gidan yari yayin da gandireba ya bindige wani baƙo har lahira

Asirin Jimmy ya fara tonuwa ne a Ughelli a jihar Delta a lokacin da ya kasa fadin wasu kalamai da ya dace kowanne kwararren likita ya sani.

Ya yi ikirarin cewa yana aiki a wani asibiti a Bayelsa hakan yasa asibitin da ke Ughelli ta fara bincike a kansa.

Buswat ya kara da cewa za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, Jimmy ya ce ya yi karatun digiri a bangaren nazarin halayen dan adam wato Psychology a Jami'ar Jihar Delta. Ya ce ya san wasu abubuwa a aikin likitoci hakan yasa ya sace takardun abokinsa, Dr Charles Umeh ba tare da saninsa ba.

KU KARANTA: An kama matar da ta damfari ɗan siyasa N2.6m da sunan za a yi amfani da 'iskokai' a taimaka masa ya ci zaɓe

A cewarsa, ya samu ilimin likitanci ne a lokacin da ya ke aiki a matsayin hadimin marigayi Dr Ajoke a Sapele. Ya kara da cewa bai taba aiki a matsayin likita ba a baya kawai ya fara ikirarin cewa shi likita ne.

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel