Twitter tana da hannu a barnar da EndSARS tayi a Najeriya, Lai Mohammed

Twitter tana da hannu a barnar da EndSARS tayi a Najeriya, Lai Mohammed

  • Lai Mohammed, ministan yada labarai yace Twitter tana da hannu a barnar da EndSARS tayi
  • Ministan ya ce Jack Dorsey ya bude asusun gudumawa ga masu zanga-zangar na gida da na ketare
  • Baya ga haka, ya dinga sake wallafa miyagun wallafar da masu zanga-zangar suka yi a lokacin

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce Twitter da mamallakinta, Jack Dorsey, suna da alhaki kan asarar da kasar nan ta tafka a yayin zanga-zangar EndSARS, daily Niegrian ta ruwaito.

Ministan ya sanar da hakan ne yayin da ya zanta da gidan rediyo Najeriya a wani shiri na ranar Talata.

KU KARANTA: Twitter ta rubutowa FG wasika, tana bukatar a tattauna kan dakatar da ita

Mohammed wanda ya zargi Jack Dorsey da tara kudin gudumawar ta Bitcoin domin daukar nauyin zanga-zangar, ya ce an yi amfani da Twitter wurin rura wutar bala'in.

Ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed
Twitter tana da hannu a barnar da EndSARS tayi a Najeriya, Lai Mohammed Hoto: punchng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Tsoho mai shekaru 56 da kifi ya hadiye kuma ya amayo shi, ya bada labari dalla-dalla

Ya yi bayanin cewa wannan zargin da yayi da farko 'yan Najeriya basu dauke shi da muhimmanci ba har sai da aka yi bincike a kai.

Kamar yadda ministan yace, an tabbatar da cewa Dorsey da kansa ya dinga sake wallafa wasu rubuce-rubuce da masu zanga-zangar suka yi.

Ya ce an sake tabbatar da cewa Dorsey ya kaddamar da wani asusu na tattara kudi da gudumawa ta Bitcoin ga masu zanga-zangar.

Ya kara da cewa shugaban Twitter ya dinga sake yada wasu wallafar da masu zanga-zangar na gida Najeriya da na kasashen ketare suka yi.

Ministan ya ce: "Idan ka ce mutane su bada gudumawa ta Bitcoin ga masu zanga-zangar EndSARS toh babu shakka kana da hannu cikin duk wata barnar da suka yi.

"Ba mu manta ba, EndSARS ta yi silar mutuwar rayuka da suka hada da 'yan sanda 37, sojoji 6, farar hula 57 tare da asarar dukiyoyi na biliyoyin naira.

"An kona motocin 'yan sanda 164, ofishin 'yan sanda 134, hukumomi masu zaman kansu 265 aka fasa aka kwashewa dukiya da kuma 243 na gwamnati.

"An balle ma'adanai 81 inda aka sace motoci sabbi sama da 200 kuma aka kone su," ya kara da cewa.

A wani labari na daban, rundunar sojin saman Najeriya, ta yi amfani da jirginta na Alpha inda ta ragargaji wuraren garin Genu dake jihar Neja, lamarin da ya kawo mutuwar wasu 'yan bindiga tare da tserewar wasu.

PRNigeria ta ruwaito cewa wasu daga cikin shanun satan da 'yan bindigan suka sato daga sansanin sojoji a jihar Katsina duk sun mutu.

Daya daga cikin bama-baman ya fada wurin liyafar biki a wani kauye dake da kusanci da garin, kamar yadda ganau suka tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng