Asari Dokubo: Abinda Fani-Kayode ya sanar da ni yayin da Nnamdi Kanu ya turo shi wurina

Asari Dokubo: Abinda Fani-Kayode ya sanar da ni yayin da Nnamdi Kanu ya turo shi wurina

  • Tsohon kwamandan tsagerun Neja Delta, Mujahid Asari Dokubo, ya bayyana yadda Nnamdi Kanu ya turo masa Fani-Kayode
  • Kamar yadda Dokubo ya bayyana, ya ce sun hadu da tsohon ministan sufurin jiragen saman a gidan gwamnatin Bayelsa
  • Nnamdi Kanu ya tura Fani-Kayode domin ya tabbatar da hadin kan mambobin IPOB da na Neja Delta domin samun Biafra

Tsohon kwamandan tsageru, Mujahid Asari Dokubo, ya bayyana yadda tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya hada shi da Nnamdi Kanu, shugaban IPOB.

A wani bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta, Asari Dokubo ya kwatanta Kanu da barawo kuma ya sha alwashin maganinsa.

Ya zargi Kanu da samun riba da fafutukar Biafra tunda bashi da takamaiman aikin yi, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Buhari ya bayyana masu daukar nauyin ta'addanci, ya sha alwashin maganinsu

Asari Dokubo: Abinda Fani-Kayode ya sanar da ni yayin da Nnamdi Kanu ya turo shi wurina
Asari Dokubo: Abinda Fani-Kayode ya sanar da ni yayin da Nnamdi Kanu ya turo shi wurina. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Sojin saman Najeriya sun yi 'yan bindiga da shanun sata luguden wuta a jihar Neja

Ya ce ya karba Fani-Kayode a gidan gwamnatin jihar Bayelsa dake Yenagoa kuma sun yi magana kan yadda IPOB zasu hada kai da tsoffin tsageru.

"Ya ku 'yan uwana 'yan Biafra, kun ji muryoyin 'yan ta'adda. Mun tambaya wadanda suka tara kudi amma ana ce mana India da Rasha, haka ne ake kididdigar kudin da aka kashe? Haka toh Biafra za ta kasance karkashin Nnamdi Kanu."

“Dan ta'adda mai suna Nnamdi Kanu yayi ikirarin cewa an turo min kudi ta wani Omiomio. Ya ce an kawo min kudi har naira miliyan 20 a Cotonou.

"Muna jiransu su kawo shaida. Sun je Cotonou sun same ni, na basu masauki kuma na ciyar dasu. Basu kawo min ko sisi ba. Akwai mutane daga wasu bangarorin Niger Delta, ba Ijaw kadai bane. Sun ci abincina kuma na biya musu wurin kwan, babu kobo da suka kawo.

“Na biya kudin asibitin mambobin IPOB a wurare daban-daban da suka samu rauni. Na sadaukar da rayuwata, na tura lauyoyi inda aka tsaresu domin kokarin fitar dasu. Mutane da yawa sun shaida hakan, amma Nnamdi Kanu barawo ne tunda yayi tunanin zai iya magana duk yadda ya so.

“Da farko, ina son tambayar Nnamdi Kani, na taba tuntubarka? Kaine ka neme ni. Mutum na farko da ka turo min shine Fani-Kayode. Ya zo kuma yace akwai bukatar mu hada kai. Ban san kuma wanda ya nema a kasar Ijaw ba amma ni dai an same ni a gidan gwamnatin Bayelsa kuma daga nan muke magana da shi," cewar Dokubo kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A wani labari na daban, Mujahid Asari Dokubo, tsohon kwamandan tsageru kuma shugaban gwamnatin gargajiya ta Biafra, ya kwatanta shugaban IPOB da zama dan ta'adda.

A wani bidiyo da ya saki a kafar sada zumunta, Dokubo ya zargi Kanu da amfani da fafutukar Biafra a matsayin wani nau'in kasuwanci.

Ya zargi Kanu da waskar da kudaden da za a yi amfani dasu domin kafa Biafra, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng