Osinbajo ya tuƙa mota mai amfani da lantarki na farko da aka ƙera a Nigeria

Osinbajo ya tuƙa mota mai amfani da lantarki na farko da aka ƙera a Nigeria

  • Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya tuƙa mota mai amfani da lantarki da aka haɗa a Nigeria
  • Osinbajo ya yaba wa waɗanda suka yi aikin haɗa motar yana mai cewa wannan na nuna cewa ba a bar Nigeria a baya ba
  • Mataimakin shugaban kasar ya tuƙa motar ne a babban birnin tarayya Abuja wurin taron baje kolin kayan da ake ƙera a Nigeria

Mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, a ranar Talata, a karo na farko ya yi tuƙin gwajin mota mai amfani da wutar lantarki da aka haɗa a Nigeria, Hyundai Kona, The Cable ta ruwaito.

A Nuwamban 2020 ne gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo Olu ya fara kaddamar da motar da kamfanin Stallion Motors ke ƙerawa.

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo
Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo yana tuka mota mai amfani da lantarki na farko da aka kera a Nigeria. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An kama hatsabibin ɓarawon da ya yi sata gidaje fiye da 1,000 a Kano

Jelani Aliyu, direkta Janar na Hukumar Tsara Motocci da Cigaba (NADDC), ya ƙaddamar da motar a watan Fabrairun 2021 a Abuja.

A ranar Talata, Osinbajo ya tuƙa motar yayin wani taro da aka yi na baje kolin kayayyakin da ake ƙerewa a Nigeria mai taken Nigeria@60 Expo da aka yi a Eagle Square a Abuja, Vanguard ta ruwaito.

A wurin taron da kwamitin Nigeria@60 da Business Visa and training Company Limited suka shirya, Osinbajo ya ce ya gamsu da abubuwan da ya gani kuma yana fatan hakan zai zama alheri ga Nigeria.

"Na ji daɗin tuƙa motar. Madallah! Hakan ya nuna za mu iya. Na yi farin cikin ganin cewa wanna mota mai amfani da lantarki ne da aka yi haɗa ta a Nigeria," in ji shi.

KU KARANTA: 'Yan bindige sun bi manajan 'stadium' har wurin aiki sun bindige shi har lahira a Jos

"Za ka iya cajin ta a ko ina, ina ganin wannan mota ce mai kyau da daɗin tuƙawa, na san hakan domin na tuƙa motar."

Pulse ta ruwaito, Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, ya ce an shirya taron ne domin baje kolin abubuwan da Nigeria ke ƙerawa da kayayyakin da ake samarwa a kasar.

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel