'Yan bindige sun bi manajan 'stadium' har wurin aiki sun bindige shi har lahira a Jos

'Yan bindige sun bi manajan 'stadium' har wurin aiki sun bindige shi har lahira a Jos

  • Yan bindiga sun halaka manaja a filin wasannin motsa jiki ta Rwang Pam, Isa Sheldat, da ke Jos, Jihar Plateasu
  • Wani wanda abin ya faru a gabansa ya ce Sheldat na zaune a gaban stadium din da rana yana hira da abokansa ne kwatsam yan bindigan suka zo a kan babur
  • Rundunar yan sanda jihar Plateau, ta bakin kakakinta Ubah Ogaba ta ce ta samu rahoton afkuwar lamarin amma tana bincike a halin yanzu

Wasu yan bindiga a ranar Talata sun bindige mataimakin manaja, Isa Sheldat, har lahira a filin wasannin motsa jiki na Rwang Pam da ke Jos, jihar Plateau kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Tribune ta ruwaito wani shaidan gani da ido, Kabiru Musa, ya shaidawa majiyar Legit.ng a ranar Talata a Jos cewa Shelda ya mutu nan take bayan harbinsa sau hudu da bindiga da maharan suka yi.

Taswirar jihar Plateau
Taswirar jihar Plateau. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Boko Haram ta sako Alooma da wasu mutum 9 da ta sace watanni 5 da suka gabata

Da ya ke bada labarin yadda abin ya faru, Musa ya ce, "Mataimakin manajan ya zo aiki a yau kamar yadda ya saba kuma yana zaune a gaban stadium da rana tare da wasu abokansa.

"A yayin da suke hirarsu, wasu yan bindiga suka sako daga kan babura suka nufi inda ya ke.

"Yana ganinsu, ya tashi zai tsere amma lokaci ya kure masa domin nan take suka bude masa wuta suka harbe shi sau hudu a kansa. Ya mutu nan take."

An gano cewa bayan wannan abin bakin cikin da ya faru, an dakatar da gasar kwallon mata da ake yi a filin wasannin motsa jikin.

KU KARANTA: An kama hatsabibin ɓarawon da ya yi sata gidaje fiye da 1,000 a Kano

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Plateau, Ubah Ogaba, ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa, "Da muka samu rahoton cewa wani abu ya faru a wurin, mun aika mutanen mu cikin gaggawa. A yanzu, ba zan iya cewa komai a kai ba domin muna kan bincike kan lamarin."

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel