Badakalar masarauta: Shugaban binciken marasa gaskiya a Kano ya ki karbar cin hancin N20m

Badakalar masarauta: Shugaban binciken marasa gaskiya a Kano ya ki karbar cin hancin N20m

- Ana binciken masarautar jihar Kano a kan zargin saida wasu filaye a Gandun Sarki

- Wasu sun ba Shugaban Hukumar sauraron korafi da binciken masu laifi, cin hanci

- Magaji Rimin Gado bai karbi cin hancin kudi Naira Miliyan 20 da aka aiko masa ba

Shugaban hukumar da ke sauraron korafin jama’a da binciken marasa gaskiya a jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya yi abinda ake ta yabonsa.

Rahotanni daga Sahelian Times sun bayyana cewa an yi wa Muhuyi Magaji Rimin Gado tayin miliyoyin kudi a matsayin cin hanci, amma ya ki karba.

Ana zargin cewa masarautar jihar Kano ce ta ba jami’in gwamnatin makudan kudi domin a dakatar da binciken da ake yi a kan badakalar wasu filaye.

KU KARANTA: Talakawa su na zargin masarauta da yunkurin sa filin idi a kasuwa

Hukumar da Muhuyi Rimin Gado yake jagoranta ta na binciken masarautar Kano a kan zargin saida wasu filaye, inda manyan fada su ka cinye kudin.

Muhuyi Magaji Rimin Gado wanda ya rantse cewa sai an gano gaskiyar wannan lamari ya nuna wasu kudi sama da Naira miliyan 20 da aka yi masa tayi.

Mutane sun fito su na ta yaba wa shugaban hukumar gwamnatin na kin karbar wadannan daloli wanda a lissafin canji sun kai kimanin Naira miliyan 24.

Hukumarsa ta tubure a kan sai ta bi diddikin hekta 22 na filayen gwamnati da aka saida a unguwar Gandun Sarki, Dorayi Karama, karamar hukumar Gwale.

Badakalar masarauta: Shugaban binciken cin-hanci ya ki karbar cin hancin N20m
Muhuyi Rimin Gado Hoto: twitter.com/baba
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin Ganduje ta na binciken Sarki Sanusi II

Rimin Gado ya na zargin cewa wasu daidaikun mutane ne su ka cika aljihunsu da kudin da aka samu bayan an saida filayen da masarautar Kano ta mallaka.

Ana zargin cewa akwai hannun wasu manya a fadar jihar Kano a wannan badakala da ake bincike.

Hakan ya sa wasu mutane da ba a bayyana su ba, su ka lallaba, su ka kawo wa shugaban wannan hukuma cin hanci domin ganin an birne binciken da ake yi.

Kwanakin baya kun ji cewa Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya fada cikin taskon zargin badakala, inda hukumar PCACC ta ke binciken fadarsa.

Ana zargin masarautar kasar Kano da yin ba daidai ba wajen saida wasu tulin filaye na gwamnati wanda rahotanni su ka ce kudinsu ya kai kimanin N1,295,000.000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng