Ana binciken Aminu Ado Bayero da Mukarrabansa da badakalar Naira Biliyan 1.3

Ana binciken Aminu Ado Bayero da Mukarrabansa da badakalar Naira Biliyan 1.3

- Hukumar PCACC ta na binciken zargin badakalar filaye a masarautar Kano

- Ana tuhumar Sarki Aminu Ado Bayero ne da karkatar da kudin wasu filaye

- Shugaban PCACC ya ce za su dauki mataki a kan wanda aka samu da laifi

Rahotanni daga jaridar Daily Nigerian sun tabbatar da cewa Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya fada cikin taskon zargin badakala.

Ana zargin masarautar kasar Kano da yin ba daidai ba wajen saida shekta 22 na filayen gwamnati wanda kudinsu ya kai kimanin N1, 295, 000, 000.

Hukumar da ke sauraron koken jama’a da zargin rashin gaskiya ta jihar Kano, PCACC, ta na binciken Sarkin da wasu manyan hadimar fadarsa.

KU KARANTA: Majalisar Kano ta na binciken Sanusi II

Jaridar ta ce Hukumar PCACC ta na zargin mai martaba da mukarrabansa da amfani da kudin filayen da su ka saida wajen yin sabgogin gabansu.

A ranar Juma’a, 2 ga watan Afrilu, 2021, shugaban PCACC, Muhuyi Magaji, ya tabbatar da cewa su na gudanar da bincike, kuma za a hukunta masu laifi.

Kafin yanzu hukumar ta gudanar da makamancin wannan bincike a kan tsohon Sarki, Malam Muhammadu Sanusi II, wanda aka tsige a shekarar bara.

Bayan Bayero ya hau gadon sarauta, ya aika takarda ta hannun gidauniyar Ado Bayero Royal City Trust Fund ya na neman amfani da wadannan filayen.

Ana binciken Aminu Ado Bayero da Mukarrabansa da badakalar Naira Biliyan 1.3
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan Aminu Ado Bayero

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, bayan Mai martaba ya samu izinin aron wannan fili, sai ya ware rabin filayen, ya yi ikirarin danginsa su ka mallaki filin

A karshe an saida bangaren filayen da dangin Mai martaba su ke da’awar na su ne a kan Naira miliyan 575, sannan aka saida ragowar a kan Naira miliyan 700.

Ana zargin cewa an biya N200m ne daga cikin kudin filin masarautar, yayin da aka karkatar da ragowar N500m, yanzu dai wannan maganar ta kai gaban hukuma.

Kwanaki aka ji Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kai ziyara zuwa kasar Ilorin, Sarkin ya ce ya koma gida ne, saboda nan ne kasar dangin mahaifiyarsa.

Aminu Ado Bayero jika ne ga sarki na takwas na Ilorin, Alhaji Abdulkadir Dan Bawa, wanda yayi rayuwa daga 1919 zuwa 1959. Danginsa ne su ke mulkin Ilorin a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel