Dalilin da ya sa aka daina bincike kan faifan daloli na Ganduje - Muhuyi Rimin Gado

Dalilin da ya sa aka daina bincike kan faifan daloli na Ganduje - Muhuyi Rimin Gado

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano, ta fayyace dalilin da ya sanya ba ta yi wani bincike ba kan zargin rashawa da a baya aka rika tuhumar gwamna Abdullahi Ganduje da shi.

Hukumar PCACC ta sanar da cewa, ba ta samu wani korafi ba hakazalika babu wasu gamsassun dalilai ko kuma hujjoji da ta samu da za su tilasta ta mayar da hankali wajen gudanar da bincike a kan zargin.

Wannan furuci ya fito ne daga bakin shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimi Gado, a yayin wata zantawa da ya yi tare da manema labarai na gidan Rediyon Freedom, mai tushe a Kanon Dabo.

A cikin hirarsa, Muhuyi ya ce tun a wancan lokaci, an shigar musu da korafi, sai dai kuma daga bisani a yayin da suka nemi karin bayani wadanda suka shigar da korafin sun yi batan dabo.

Muhuyi ya ce sun nemi karin bayani da jin ta bakin masu korafin amma ba su samu nasarar samunsu, lamarin da ya wajabta musu watsi da lamarin.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje
Hakkin mallakar hoto; Fadar gwamnatin Kano
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje Hakkin mallakar hoto; Fadar gwamnatin Kano
Asali: Twitter

A yayin jaddada tsayuwar dakan hukumar da ya ke jagoranta wajen sauke nauyin da rataya wuyanta, Muhuyi ya ce babu wanda ya sha gaban doka kuma har a yanzu sun gudanar da bincike kan manyan jami'an gwamnati da dama.

"Mun gudanar da bincike kan manyan jami'an gwamnati bayan da muka sami korafi a kansu."

Wannan tattaunawa da Muhuyi da gidan Rediyon Freedom ta zo ne kwanaki kadan bayan da aka yi musayar yawu kan zaben gwamnan Edo tsakanin Ganduje da takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike.

A yayin da Ganduje ya kasance jagoran kwamitin yakin neman zaben gwamnan Edo na jam'iyyar APC, ita kuwa jam'iyar adawa ta PDP ta zabi Wike ya rike akalar yakinta na neman zaben gwamnan jihar.

KARANTA KUMA: Jagoran mafarautan Borno ya fada tarkon garkuwa ta 'yan Boko Haram

Lamari na baki ya san mai zai furta amma bai san me za a mayar masa ba, ya sanya Ganduje cikin barkwanci ya ce zai killace Wike har sai an gama zaben gwamnan na Edo.

Shi kuwa Wike a yayin mayar da martani, ya shaidawa Ganduje cewa shi ba daloli bane balantana ya sunkuma shi cikin aljihun babbar riga.

Legit.ng ta tuna cewa a shekarar 2018 ne wasu faifayen bidiyo suka billo masu hasko Ganduje yana zuba daloli a aljihu wanda aka ruwaito cewa na goro ne ya karba daga hannun masu aikin kwangila.

An gano gwamnan yana karban daloli yana zubawa a cikin babban rigansa, wannan ya haddasa alamomin tambaya a watanni da dama da suka gabata.

Wata kafar sadarwa ta Najeriya wadda ta fara wallafa bidiyon, ta ce jimillar kudin da Ganduje ya rika jefa wa cikin aljihu sun kai dala 230,000, kimanin naira miliyan biyar kenan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel