An gano mangwaro mai ‘fuskan mutum’ a jikin bishiya, jama’a sun yi tururuwan zuwa kallo a wani bidiyo

An gano mangwaro mai ‘fuskan mutum’ a jikin bishiya, jama’a sun yi tururuwan zuwa kallo a wani bidiyo

  • Jama’a sun cika da mamaki yayin da aka gano wani mangwaro mai kamannin fuskan mutum a jikin wani bishiya
  • Mazauna yankin da suka cika da al’ajabi sun zagaye bishiyan domin ganin dan itacen mai ban tsoro yayinda wasu da dama suka dauki hotuna da bidiyonsa
  • Wani bidiyo da ya bayyana daga wajen ya haddasa cecekuce a shafukan soshiyal midiya

Al’umman wani gari da ba a bayyana ba sun nuna wani dan itacen mai ban al’ajabi da suka gano. Mazauna garin a cikin wani bidiyo da ya bayyana sun gano mangwaro mai kamannin fuskar mutum a jikin wani bishiya.

A wani bidiyon da @kingtundeednut ya wallafa a Instagram, an gano mutanen kewaye da bishiyan da dan itacen yake yayinda suke daukar hotuna da bidiyon.

KU KARANTA KUMA: 12 ga watan Yuni: Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga a Lagas

An gano mangwaro mai ‘fuskan mutum’ a jikin bishiya, jama’a sun yi tururuwan zuwa kallo a wani bidiyo
Jama'a sun gano mangwaro mai dauke da kamannin fuskan mutun Hoto: @kingtundeednut
Asali: Instagram

An gano koren magwaron da launin dorawa a jikinsa.

‘Yan Najeriya sun yi martani kan mangwaron

Masu amfani da shafukan soshiyal midiya sun karbi labarin da martani mabanbanta. Wasu sun yi kokarin bayyana dalilin da yasa dan itatuwan ke da suffan mutum yayinda abun ya ba wasu mamaki.

@scoobynero ya rubuta:

“Mangwaron da ya isa ci!!! Haka za su bar shi a wajen har ya nuna, ya fadi sannan ya rube.”

@therealfatfact ya ce:

“Kila ma wani ne yayi hakan da daddare Sannan shi din kuma ya kira mutane da safe don su zo su gani.”

@gabriel.ejike ya bayyana:

“Na shiga rudani me ya faru me yasa suke daukan mangwaron.”

A wani labarin, diyar mai kudin Najeriya, Aliko Dangote, Halima ta shiga kanen labarai kuma ta birge masu amfani da shafukan intanet.

Matashiyar matar wacce kan birge masoya da rashin hayaniyarta ta ba mutane da dama mamaki bayan ta fito ta yi rawa a wani taro da ta halarta.

Sabanin yadda aka saba ganinta, matashiyar ta sha rawa a filin taro yayinda take rera wakar da ke tashi na shahararriyar mawakiya, Teni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel