Buhari ya bayyana masu daukar nauyin ta'addanci, ya sha alwashin maganinsu

Buhari ya bayyana masu daukar nauyin ta'addanci, ya sha alwashin maganinsu

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace masu kudi da wadanda yanzu gwamnati bata damawa da su ne ke daukar nauyin ta'addanci

- Buhari yace babu sassauci balle daga kafa ga duk wanda aka kama yana daukar nauyin ta'addanci, dole ne ya fuskanci shari'a

- Shugaban kasa ya sha alwashin mika mulki a yayin da kasar ke ganiyar cigaba a fannin arziki da tsaro

Shugaban kasa Muhammaadu Buhari yace masu daukar nauyin ta'addanci a kasar nan suna neman dacewa ne.

Shugaban kasan ya sanar da hakan a ranar Juma'a yayin tattaunawa da gidan talabijin na kasa (NTA).

Buhari ya ce duk wanda aka kama da hannu cikin daukar nauyin ta'addanci a kasar nan zai dandana kudarsa kuma dole ne ya fuskanci shari'a.

Ya ce da yawa daga cikin masu daukar nauyin ta'addanci mutane ne masu kudi da kuma wadanda a halin yanzu basu cikin gwamnati.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari zai yi tattaunawa ta musamman da NTA a yammacin Juma'a

Buhari ya bayyana masu daukar nauyin ta'addanci, ya sha alwashin maganinsu
Buhari ya bayyana masu daukar nauyin ta'addanci, ya sha alwashin maganinsu. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kaduna: Hukumar foliteknik ta Nuhu Bamalli ta rufe makarantar bayan satar dalibai da Malamai

Shugaban kasan yace ba a yi masa adalci ba a kasar nan idan aka ce ya bar 'yan bindiga suna cin karensu babu babbaka.

Ya kara da cewa da yawa 'yan Najeriya sun fahimcesa kuma suna godewa akan irin kokarin da yake yi na ganin tsaron kasar nan ya tabbata.

Shugaban kasan yace burinsa shine ya bar Najeriya cike da cigaban da bai tarar ba yayin da ya sameta.

"Ina son mika kasa mai arziki, tsaro da isa idan na tashi barin mulki," yace.

Ya kara jaddada cewa dole ne matasa su bada goyon baya ga gwamnatinsa wurin inganta tsaron kasar nan.

"Jin dadinku ne tabbatar da tsaron Najeriya," Shugaban kasan yace yayin jawabi ga matasa.

A wani labari na daban, Alhaji Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, ya kare gwamnatin tarayya kan yadda ta dakatar da al'amuran Twitter a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Yau mako daya cif kenan da Mohammed ya sanar da hukuncin da gwamnatin tarayya ta yankewa Twitter bayan an zargesu da katsalandan a al'amuran kasar nan.

Tun bayan nan, jama'a sun matsantawa gwamnatin tarayya domin ta dage dokar haramta Twitter. A yayin jawabi a wani shiri a NTA na ranar Juma'a, Mohammed ya zargi Twitter da barin Nnamdi Kanu, shugaban IPOB da cin karensu babu babbaka, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng